Yanzu lokaci ne na yi wa Zamfara aiki bilhaƙƙi, cewar Gwamna Dauda ga ‘yan majalisar jihar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira ga sabbin ‘yan Majalisar Dokokin jihar da su haɗe kai da yin aiki tare don cigaban jihar.

Lawal ya yi wannan kira ne yayin ganawar da ya yi da sabbin mambobin majalisar a zauren Majalisar a ranar Talata.

A ranar Talata ta wannan makon aka rantsar da ‘yan majalisar Jihar Zamfara karo na bakwai.

Sanarwa da mai bai wa Gwamna Dauda shawara kan lamurran yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Laraba ta ce, Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki ne aka zaɓa a matsayin Shugaban Majalisar ba tare da hamayya ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamnan ya karɓi baƙuncin shugabancin Majalisar karo na bakwai ne don sani da kuma fahimtar juna.

Kazalika, Gwamnan ya yi kira ga ‘yan majalisar da su yi aiki kafaɗa-da-kafaɗa da majalisar zartwar don cigaban gwamnatin jihar.

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen taya murna ga ‘yan majaisar su 24 da aka rantsar a yau.

“Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatina a zaƙe take don haɗa kai da majalisar dokokin jihar, kuma dole mu dunƙule mu yi aiki tare domin tabbatar da ƙawancenmu.

“Zamfara na fuskantar matsaloli masu ƙarfin gaske, kama daga matsalar tsaro zuwa taɓarɓarewar tsarin ilimi da sauransu.

“Siyasa ta wuce, yanzu lokaci ne da ya kamata a haɗe kai a yi wa Jihar Zamfara aiki bilhaƙƙi, in ji Gwamnan.

Tun farko da yake jawabi, Shugaban Majalisar, Hon. Bilyaminu Ibrahim Moriki, ya ce, ‘yan majalisar za su bai wa ɓangaren zartarwa cikakken haɗin kai da goyon baya don ci gaban jihar.