Daga BELLO A. BABAJI
Cikin wani saƙo da ofishin ya wallafa a shafinsa na X, ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:09 na ranar Laraba.
Wannan shi ne karo na 12 cikin shekarar 2024 da irin hakan ke faruwa.
Acikin saƙon, ofishin ya ce nan ba da jimawa za a fara aikin gyara a kai.
Haka ma kamfanin raba wutar lantarki na Jos ya fitar da sanarwa game da batun inda ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:33 na rana wanda hakan ya sanya kwastomominsa suka rasa wuta, kamar yadda Kakakin Kamfanin, Dakta Friday Elijah ya bayyana.