Yanzu-yanzu: Emefiele ya sake ƙin amincewa da tuhumar EFCC a kotu

Hukumar yaƙi da rashawa ta (EFCC), ta sake gurfanar da tsohon Shugaban Babban Bakin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele a kotu bisa zargin ba da damar buga Naira miliyan 684.5 a kan Naira biliyan 18.96 da sauransu.

Da yake jawabi a gaban Alƙali Maryann Anenihna Babbar Kotun Abuja, Emefiele ya ce sam bai yarda da zarge-zarge huɗun da EFCC ke tuhumarsa ba.

EFCC ta yi zargi Emefiele ya saɓa wa doka da gangar da nufin yi wa al’umma illa a lokacin da ya aiwatar da canjin kuɗi a matsayinsa na Shugaban CBN a tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Haka nan, hukumar na zargin Emefiele da cire biliyan N124.8 daga asusun tara haraji na gwamnatin ƙasa ta haramtacciyar hanya.

Yayin gurfanar da tsohon Shugaban CBN da aka yi a ranar Laraba, an bijiro da ragowar tuhuma guda ukun da ake yi wa Emefiele ɗin ne.