Yanzu-yanzu: Gwamnati ta ƙara kuɗin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC) ta ba da umarnin gaggawa kan ƙarin kuɗin wutar lantarki daga ranar Laraba, 3 ga watan Afrilun da ake ciki.

Mataimakin Shugaban hukumar NERC, Musiliu Oseni ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Oseni ya ce ƙarin ya shafi kashi 15 na adadin masu amfani da wutar lantarki ne wanda kuma su ne ke shan kashi 40 na wutar da ake samarwa baki ɗaya.

Ko a watan Janairun da ya gabata, NERC ta ce gwamnatin Nijeriya za ta biya Naira tiriliyan 1.6 don tallafa wa ‘yan ƙasar game da wutar lantarkin da za su sha a 2024.