Yanzu-yanzu: Shugaban Ƙasar Iran ya rasu yana da shekara 63

Rahotanni daga ƙasar Iran sun tabbatar da mutuwar Shugaba Ebrahim Raisi na ƙasar sakamakon hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

An ce jirgin saman ya yi hatsari ne sakamkon rashin kyawun yanayi.

Marigayin ya bar duniya yana da shekara 63.

Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce an ga buraguzan jirgin a cikin wasu tsaunuka masu sarƙaƙiya.

Shugaban ƙungiyar agaji ta Red Crescent a Iran, ya ce masu aikin ceto sun isa wurin da suka ga ɓuraguzan jirgin sai dai babu alamar akwai waɗanda suka tsira.

Bayanai sun ce jirgin na ɗauke ne da Shugaba Ibrahim Raisi da ministan harkokin wajensa, da wasu mutane da ba a san adadinsu ba.

A Lahadin da ta gabata aka rawaito jirgin sama mai saukar ungulu ɗauke da Shugaban Iran da ministan harkokin wajen ƙasar ya yi hatsari a wani yanki mai tsaunuka da ke Arewa maso yammancin ƙasar.