Yanzu-yanzu: Shugaban PDP na Abuja ya mutu a haɗarin mota

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, a babban birnin tarayya Abuja, Sunday Dogo Zaka ya rasu.

Blueprint Manhaja ta samu labarin cewa, Zaka ya mutu sa’o’i kaɗan kafin zaɓen Shugaban Ƙasa da ake gudanarwa a yau Asabar a wani hatsarin da ya rutsa da shi a ƙaramar hukumar Kuje.

Kamar yadda wata majiya ta kusa, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana, motar Zaka ta yi karo da falwayar wutar lantarki a kusa da gidansa da ke Kuje a lokacin da yake dawowa daga ganawa da Sanata Philip Aduda da misalin ƙarfe 3 na safiyar Asabar.

Manhaja ta tattaro cewa, Zaka na tare da wani makusancinsa a cikin motar, wanda shi ma ya mutu a hatsarin yayin da aka tabbatar da mutuwar Zaka a wani asibiti da ke Kuje.

Majiyar ta ce, “Baƙar rana ce da PDP ta rasa shugabanta na Abuja, Zaka Sunday Dogo.

“Motar sa ta yi karo da falwaya ta wutar lantarki a lokacin da yake dawowa daga ganawa da Sanata Aduda da sanyin safiyar yau.

“Yana tare da wani abokinsa a cikin motar wanda ba mu san ko waye ba tukunna, amma abokin ya mutu nan take.

“Mutane sun taru a gidansa na Kuje yayin da nake magana da ku. Wannan babbar illa ce ga ‘yan PDP a Abuja,” inji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *