‘Yar gwagwarmaya, Naja’atu ta daina siyasar jam’iyya

Daga BASHIR ISAH

Darakta a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, Naja’atu Bala Muhammad, ta yi murabus daga matsayinta.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kimanin wata ɗaya kafin babban zaɓen 2023.

A cikin wasiƙar murabus da ta miƙa wa Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, Naja’atu ta koka kan yadda harkokin siyas ke gudana a ƙasar.

Wanda a cewarta hakan ya sa ta ga ba za ta iya ci gaba da zama a cikin harkar siyasar jam’iyya ba.

“Ƙalubalan da Nijeriya ke fuskanta a yau ya sa ni ci gaba da gwagwarmaya da kyakkyawar niya don samun maslaha, kuma zan ci gaba da zama mai biyayya ga Nijeriya,” in ji ta.

Ta ce ta zaɓi ficewa ne bayan da ta fahimci tafiyar jam’iyyar ta saɓa wa aƙidarta.

Ta ƙara da cewa, ta fahimci babu wani bambanci a tsakanin jam’iyyun siyasa, saboda ‘yan siyasa ba su da wani buri da ya wuci cim ma burika da buƙatun kansu.

“Ƙoƙarina shi ne mara wa waɗanda suke da kyakkyawar niya ta ganin an mangance matsalolin ƙasa. Kuma don ci gaba da tabbata kan wannan turba dole ya zamana mutum na iya ɗaukar matakin da ya dace,” in ji ‘yar gwagwarmayar.

Ta nuna takaicinta dangane da yadda matsalolin rashin tsaro da talauci da sauransu ke ci gaba da ci wa ‘yan ƙasa tuwo a ƙwarya.

Ta shawarci ‘yan Nijeriya da su san sakamakon da zai biyo baya idan suka yi zaɓen tumun dare a 2023.

A Nuwamban 2022 ‘yar gwagwarmayar ta yi kira da a hukunta matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, kan badaƙalar tsare ɗalibin nan Aminu Mohammed da ke Jami’ar Tarayya a Bauchi.