‘Yar jaridar ta yi ɓatan-dabo bayan an ba da belinta a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Kawo yanzu ba a san inda Ruƙayya Aliyu Jibiya take ɓoye ba, tun bayan da Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Katsina ta tsare ‘yar jaridar wadda ta kasance wakiliyar tashar Tambarin Hausa, bisa zarginta da cin mutuncinsu a shafinta na TikTok.

Rundunar ‘Yan Sandan jihar ce ta kama ‘yar jaridar ta kuma tsare ta bisa sukar lamirin ‘yan sanda.

Tun farko Blueprint Manhaja ta bayyana cewar Ruqayya ta wallafa wata bidiyo a shafinta na Tiktok, inda ta ƙalubalanci ‘yan sanda a jihar bayan da suka kama wasu mata masu zaman kansu a ɗaya daga cikin otal-otal da ke jihar, aka kuma kira taron manema labarai inda rundunar ta nuna su ga ‘yan jarida gami da zargin su da aikata sana’ar karuwanci.

A cikin bidiyon, Ruqayya ta ƙalubalanci ‘yan sandan, inda ta nuna cewa nuna fuskokin matan a bainar jama’a tamkar cin zarafi ne a gare su, kuma an take haƙƙinsu a matsayinsu na ‘yan Nijeriya.

Ta kuma buƙace su a kan su daina bayyana fuskokin masu laifi a bainar jama’a har sai kotu ta tabbatar da laifinsu.

Lamarin da bai yi wa rundunar daɗi ba, inda suka cafke Ruƙayya suka kuma tsare ta, sai dai daga baya sun miƙa ta kotu, amma sakamakon rashin zuwan alƙalin da zai saurari tuhumar da ‘yan sanda ke wa ‘yar jaridar sai aka bayar da ita beli bisa sharaɗin za ta sake komawa kotun idan alƙali ya dawo.

Ta kuma ce daga bisani, ‘yan sandan sun buƙace ta da ta kai kanta hedikwatar rundunar, domin ganawa da Kwamishinan ‘yan sandan jihar.

A wani sabon bidiyo da Ruƙayya ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ta ƙi zuwa hedikwatar rundunar ne sakamakon mai kare ta baya nan, ba ta kuma san abun da zai faru tsakaninta da ‘yan sandan ba.

“Na gudu na ɓoye saboda lauyana ba ya nan kuma ban san me ‘yan sanda za su yi mini ba a kan maganar da na yi, wacce ba ta da illa kuma ina da damar da zan yi ta amma ga abunda ya faru.

“Saboda haka na ruga na ɓoye saboda rayuwata,” inji ta.

‘Yar jaridar ta kuma ce a halin yanzu rayuwarta na cikin hatsari
shi ya sa ta ɓoye kanta saboda ana mata barazana.