‘Yar Nijeriya ta zama baƙar fata ta farko da ta lashe shugabancin jam’iyyar Conservative a Ingila

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohuwar Sakatariyar Kasuwanci ta ƙasar Ingila, Kemi Badenoch ta zama sabuwar shugabar jam’iyyar Conservative bayan doke Robert Jenrick da ta yi a zagaye na ƙarshe a zaɓen da suka kara a ƙasar.

Badenoch, wacce ta girma ne a Nijeriya, ta zama baƙar mace ta farko da ta samu shugabancin babbar jami’yya a ƙasar Turai.

Za ta karɓi ragamar jagorancin jam’iyyar ne inda za ta gaji Rishi Sunak bayan ta samun ƙuri’u 53,806 inda abokin karawarta, Jenrick ya samu ƙuri’u 41,388.

Tsohon Sakataren Shari’a, Robert Buckland ya ce Misis Badenoch ƙwararriya ce da za a ji dadin aiki tare da ita saboda ƙoƙarinta a wasu harkokin gwamnati.

A lokacin da ta ke magana game da nasarar, Badenoch ta ce yanzu lokaci ne na a fara aiki a Tarayyar Turai inda ta ce za ta yi iya yinta wajen sauƙe nauye-nauyen da aka ɗora mata.

An dai haifi sabuwar shugabar jam’iyyar ne a shekarar 1980 a Landan wadda iyayenta asalin ƴan ƙabilar Yarbawa ne. Ta fara tasowa ne a Amurka da Legas inda daga bisani ta koma Turai a lokacin da ta ke da shekaru 16 a duniya.