Daga BASHIR ISAH
‘Yan sanda a jihar Adamawa sun kama wata budurwa ‘yar shekara 18 mai suna Blessing John, a daidai lokacin da ta yi yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da ta sato.
Da take yi wa ‘yan sanda bayani, Blessing ta amsa cewa ta ƙwamuso yaron ne a Michila da nufin kai shi Mubi ta sayar don ta samu kuɗin sayen gida da mota. Blessing ‘yar Unguwan Cashew da ke hanyar Babban Asibitin Michika ce.
Bayanan ‘yan sanda sun nuna Blessing ta yaudari yaron ne ta ɗauke shi daga Michika zuwa Anguwan Kara da ke Mubi don miƙa shi ga wanda suka shirya zai saye shi. Tare da cewa, ganin dukkan ƙoƙarin da ta yi na kiran wanda zai sayi yaron a waya ya ci tura, shi ya sa cikin zaƙuwa ta shiga tambayar inda za ta ga mutumin da take nema, inda a nan ta yi suɓul-da-bakan cewa ta kawo masa yaro ne don ya saya.
Daga bisani bayanin haka ya isa kunnen ofishin ‘yan sanda inda jami’ai suka shiga suka kamo Blessing, in ji mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Sulaiman Nguroje.
Nguroje ya ce yarinyar ta ƙulla alaƙa da wani mai garkuwa ne a lokacin da ta ziyarci wata ƙawarta Mubi wadda ta hure mata kunne kan cewa za ta samu kuɗi ta hanyar nemo wa matsafa yara suna saye.
A ƙarshe, Nguroji ya ja hankalin iyaye da su maida hankali sosai a kan ‘ya’yansu da kuma tantance irin abokan da suke mu’amala da su.