Yari da Marafa sun sauya sheƙa zuwa PDP

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwmanan Jihar Zamfara, Abdul’azeez Yari tare da wasu jiga-jigan APC a jihar irin su Sanata Kabiru Marafa da sauransu haɗe da magoya bayansu, sun sauya sheƙa zuwa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.

Shugaban PDP na jihar, Bala Mande ne ya bayyana hakan sa’ilin da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi.

Da yake jawabi Mande ya ce, “’Yan jarida, mun kira ku ne don mu shaida muku cewa tsohon Gwamnan Zamfara, Alhaji Abdul Aziz Yari da Sanata Kabiru Garba Mafara da danzon magoya bayansu sun dawo PDP.

“Sun shigo cikinmu, kuma mun cim ma yarjejeniyar da za mu aiwatar da ita.”

Mande ya ƙara da cewa, nan ba da daɗewa ba za a yi bikin karɓar Yari da sauransu zuwa PDP a hukumance a Gusau babban birnin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *