Yari, Marafa da Sahabi sun lashe zaɓe ƙarƙashin APC

Daga SANUSI MUHAMMAD a
Gusau.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, Sanata Kabiru Garba Marafa da kuma Sanata Sahabi Ya’u a yau sun lashe zaɓen zama yantakarar majalisar dattawa ƙarƙashin Jam’iyyar APC.

Zaɓen da aka gudanar cikin lumana ya samu halartar Gwamna Bello Mohammed Matawalle.

Tsohon gwamnan Abdulaziz Yari ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, India yasamu ƙuri’u 306 ƙuri’u daga cikin wakilai 310 da suka fito daga mazaɓu 62 a yankin.

Hakazalika, zaɓen an gudanar da shi lokaci guda a adadin yankunan majalisar dattawa uku dake jihar.

Bayan haka, shugaban majalisar dokoki jihar, Alhaji Nasiru Mu’azu Magarya ya jagoranci zaɓen a Ƙaura Namoda yankin Ɗan Majalisar Dattawa ta Arewa, da mataimakin gwamnan jihar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha halarci zaɓen a yankin Zamfara ta tsakiya.

Anasa jawabin, Shugaban Jam’iyyar APC ta Jihar, Hon. Tukur Umar Danfulani ya nuna gamsuwa da yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana.

Hakazalika gwamna Bello Mohammed Matawalle yayi godiya ga Allah bisa hadin kai ya dawo a tsakanin jigajigan mambon jam’iyyar APC a Jihar tare yabawa bisa yadda zaɓukan fidda gwanin ya gudana tun daga matakin gwamna, ‘yan majalisar jiha, wakilai da dattawa cikin lumana da nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *