Yari ya ƙalubalanci shugabancin APC na ƙasa game da rusa shugabannin APC na Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Tsohon Gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari Abubakar, ya ƙalubalanci shugaban kwamitin riƙo na ƙasa na Jami’iyyar APC, Alhaji Maimala Buni a kan rusa shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, yana mai bayyana matakin na Maimala Buni da cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulkin APC.

Yari ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a gidansa da ke garin Talata Mafara, hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar a ranar Juma’a.

A cewarsa, shugabancin APC na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Alhaji Maimala Buni ba shi da wata halastacciyar dama ta rusa shugabannin jam’iyyar APC na jihar wanda ya gudanar tun daga mazaɓu, kansilolin ƙananan hukumomi da mataki jiha a sakamakon komawar Gwamnan Zamfara jam’iyyar APC a kwanakin baya.

“Na yi tsammanin shugabancin kwamitin rikon na kasa na Jami’iyyarmu ta APC, ƙarkashin jagorancin Alhaji Maimala Buni za su mutunta kundin tsarin mulkin jam’iyyar APC da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari wanda a kodayaushe yake ba da shawarar buƙatar mutunta dokoki amma ya yi biris da shi”, in ji Yari.

Ya danganta hukuncin da shugaban kwamitin riƙon na kasa na jam’iyyar APC Alhaji Maimala Buni ya ɗauka a matsayin rashin cancanta, rashin bin tsarin mulki da kuma bin tsarin dimokuraɗiyya.

Ya ce, “A gaskiya ba mu amince da matakin da shugaban kwamitin riƙon na ƙasa Alhaji Maimala Buni ya yanke ba na rusa shugabannin jam’iyyar da muke da su na APC tun daga mazaɓu, ƙananan hukumomi da kuma matakin jihohi, kuma mun yi Allah wadai da matakin.”

Ya ci gaba da cewa zai ci gaba da kasancewa a jam’iyyar APC, kuma ya yi maraba da Gwamna Bello Mohammed Matawalle don komawa APC a jihar, tare da yin kira ga Matawalle da ya yi taka tsantsan game da waɗanda za su kawo ƙiyayya da aiwatar da manufofin tsakanin mambobin APC, kana ya yi kira ga magoya bayansa su kasance masu nutsuwa da bin doka da oda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *