Yariman Saudiyya ya yi alƙawarin tallafa wa canjin da Tinubu ke yi a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI

Yariman Saudiyya kuma Firaministan ƙasar, Muhammad bin Salman bin Abdul’aziz Al Sa’ud ya tabbatar da cewa zai tallafa wa Nijeriya a ƙoƙarinta na gyare-gyaren harkokin tattali.

Hakan na zuwa ne a lokacin da Yariman da Shugaba Bola Tinubu suka haɗu a Riyadh dake Saudiyya a yayin taron ƙasashen Musulmai Larabawa.

Manyan ƙasashen biyu sun tattauna kan ɓangarorin haɗaka da suka haɗa da mai, gas, noma da ababen rayuwa da kuma samar da Majalisar Kasuwanci ta Saudi-Nijeraya wanda za a zuba aƙalla Dala biliyan 5.

A shekarar 2022 ne kamfanin noma da kiwo na Saudiyya (SALIC) ya zuba Dala biliyan 1.24 don sayen hannun-jari a babban kamfanin harkar noma na Nijeriya mai suna Olam Agric inda ya mallaki kaso 35.43.

Yariman ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan ƙoƙarinsa na samar da sauye-sauye a ɓangaren tattalin arziƙin Nijeriya, ya na mai cewa zai bada gagarumar gudummawa wajen bunƙasa ƙasar.