Daga AMINA YUSUF ALI
A lokacin da Ƙasar Faransa ke shirin bayar da mulki ga ƙasashen Afrika da ta mulka, ta ƙulla wasu yarjeniyoyi guda 11 tsakaninta da ƙasashen, waɗanda a yanzu ke zama tarnaƙi ga ɗorewar ɗiyaucinsu.
Da ma akwai yarjejeniyar da ta haramta ƙasashen rainon Faransa guda 14 ikon haɗin gwiwa na sojoji da wata ƙasar kuma an haramta musu ikon sayen kayan yaƙi a wata ƙasa ta Turai ba tare da sahalewar ƙasar Faransa ba.
Wasu daga cikin ƙasashen Afirka da Faransa ta raina sun haxa da: Mauritania, Senegal, Mali, Guinea, Ivory Coast, Burkina Faso, Benin, Nijar, Chadi, Kamaru, Afirka ta tsakiya da DR Congo.
Ga yarjejeniyar kamar haka:
- Nauyi ƙasar ne da ta sauke dukka romon mulkin ga ƙasashen da take raina.
- Ikon ƙwace tanadin kuxin qasa kai tsaye.
- Ikon farko na ƙin amincewa da duk wani kayan aiki ko alabrkatun ƙasa da aka samu a ƙasar.
- Fifta buƙatun Faransa da kamfanoninta a kan sha’anin al’umma da yanayin halastaccen kuɗin ƙasa.
- Kevabtaccen iko na samar da kayan yaƙi da bayar da horaswa ga jami’an sojin ƙasar da suke raina.
- Faransa tana da damar samar da sojoji don yin kutse ta yi amfani da ƙarfin soja don kare muradunta a ƙasashen da take raina.
- Wajibcin sanya harshen Faransanci ya zama harshen hukuma na ƙasar kuma harshen da za a yi amfani da shi a makarantun ƙasar.
- Wajibcin amfani da Saifa/CFA (Kuɗin ƙasar Faransa) a ƙasashen Afirka rainon Faransa.
- Wajibi ne a aika wa da Faransa takardar lissafin shekara tare da rahoton kuɗaɗen da ƙasar ta adana ba tare da an ba da rahoto ko kuɗin ba.
- A rushe duk wata alaƙar soji da wasu ƙasashen sai dai idan Faransa ce ta ba da damar haka.
- Tilas kuma su mara wa Faransa baya a duk wani lokaci da yaƙi ko rikici ya ɓarke a duniya.