Yau kotu za ta yanke hukunci kan ƙarar da ASUU ta ɗaukaka

Daga WAKILINMU

Wannan Juma’ar ake sa ran Kotun Daukaka Kara za ta yanke hukuncin kan buƙatar da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) na jingine umarnin da Kotun Ma’aikata ta ba ta na ta janye yajin aikin da take yi.

Ganin ba ta gamsu da umarnin da Kotun Ma’aikatan ta bayar kan malaman jami’o’i su koma bakin aiki ba, ya sanya ASUU garzayawa Kotun Ɗaukaka Ƙara don ci gaba da neman buƙatunta a wajen gwamnati.

Lauyan ASUU, Femi Falana (SAN), ya ce daidai ne ɗaukaka kara da ƙungiyar ta yi kan umarnin kotun, saboda a cewarsa, umarnin ya saba mata.

Falana ya buƙaci Kotun Ɗaukaka Ƙarar ƙarƙashin Mai Shari’a Hamma Barka, da ta janyen adawar gwamnatin ga buƙatar daukaka karar da ASUU ta shigar kotu.

Jaridar Aminiya ta rawaito lauya Falana na cewa, abu ne mai hatsari hana wanda yake karewa (ASUU) ɗaukaka ƙara zuwa gaba.