Yau ta ke Ƙaramar Sallah a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa, ya samu sahihan rahotanni daga sassan Nijeriya dangane da ganin watan Ƙaramar Sallah na bana.

Don haka yau Juma’a ta ke 1 ga Shawwal, 1444 AH, wanda ya zo daidai da 21 ga Afrilu, 2023.

Kwamitin tantance ganin wata ƙarƙashin jagorancin Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan.

An buƙaci Musulmai masu aminci a Nijeriya da su bi ƙa’idojin COVID-19 yayin bikin sallar.

Sarkin ya kuma buƙaci al’ummar Musulmi da su yi wa ƙasar nan addu’ar zaman lafiya da haɗin kai, inda ya jaddada muhimmancin soyayya, tausayi da gafara a matsayin muhimman ginshiƙan addinin Musulunci.

Ya kuma buƙaci al’ummar Nijeriya da su yi wa sabbin shugabannin da aka zaɓa addu’ar Allah Ya ba su damar gudanar da shugabanci nagari tare da yi wa ƙasar addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Ƙasar Saudiyya da wasu ƙasashen Daular Larabawa su ma tuni suka sanar da yau Juma’a ita ce 1 ga watan Shawwal, inda za su gudanar da Eidil Fitr ɗin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *