
Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Wannan na ɗaya daga cikin abubuwa da musulmi su ka sami rarrabuwar kai tsawon zamunna a tarihin musulunci zuwa yanzu. Yayin da Ahlul Sunnah ke ajiye azumi bayan faɗuwar rana, ƴan Shi’a kuma sai duhu ya bayyana.
Kowanne ɓangare ya na da wata madogara, domin dai Ahlul Sunnah sun kafa hujja da hadisin Bukhari na 1091, wanda aka ruwaito Annabi ya ce, “Idan Rana ta faɗi, lokacin buɗe baki ya yi.”
Su kuma Yan Shia sai su ka kafa hujja da ayar Ƙur’ani cikin Q17:78 “Ka tsayar da salla a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare da lõkacin fitar alfijir lalle ne karãtun fitar alfijir ya kasance wanda ake halarta.”
Wannan aya sai Imam Jafar Sadiq ya fassara ta cikin Al-Kafi cewa bayan taurari sun bayyana. Shi ma Imam Baqir a Ta’adhib Al Ahkam haka ya yi fassarar, abinda ya sa Shi’a su ka dauki yin bude-baki bayan duhu ya yi.
To akwai abubuwan lura guda biyu dangane da wannan aya, na farko dai ba kai-tsaye ta ke magana a kan buɗe-baki ba, amma kuma a fakaice tunda ta na maganar sallar magariba ne, kaga akwai alaka da buɗe-baki domin kowa ya yarda cewa a lokacin buɗe-baki ake sallar magariba.
Abu na biyu shine “Dulukil shamsi ila gasakil laili” wato karkatar Rana zuwa ga duhun dare, za a iya fassarawa da ɓacewar Rana ta koma sashen dare, yadda ba a iya ganinta a sama kafin ainihin duhu ya shiga. Ko kuma a dauka bayan ta bace din sai duhu ya shiga yadda za a ga taurari, kamar yadda Imam Jafar ya fassara.
Idan da mu na yiwa juna uzuri, duk waɗannan fahimta daidai ne domin ayar ta bada hurumin fahimta mabanbanta. Sunna na iya riƙo da wancan hadisi, Shi’a na iya riƙo da fahimtar fassarar wannan aya. Matsalarmu gaba ɗaya ita ce, fahimta ta ita kadai ce fahimta, ta wani ba daidai ba ce.
Ga wanda ya yi nazarin kimiyyar Geography na Duniya, wannan matsala ba matsala ba ce, domin Allah da ya halicci duniyar, sai ya yi ta yadda yankuna mabanbanta su ke da gagarumin banbanci tsakaninsu na yanayin dare da yini, yadda ba za ka iya bada wata fassara ƙwaya ɗaya wadda za ta gamsar da dukkan sassan ba.
Misali idan ka tafi ƙasashen da ke ƙuryar doron Duniya na Arewa, musamman a Arctic Circle, za ka samu a wajajen watan June, abinda ake kira da Summer Solstice, da lokacin Winter Solstice wajen December, ake samun Rana ba ta ma faɗuwa kwata-kwata ko kuma ba ta fitowa kwata kwata. A ɓangaren Alaska, Antarctica da Greenland, akwai lokacin da Rana ke kusan watanni shida ba ta faɗi ba, ko kuma a yi watanni shida ba ta fito ba, wato jiddin a cikin dare ake.
Shin musulmi a waɗannan yankuna, ta yaya za su yi Sahur da buɗe-baki? Wannan na ɗaya daga cikin hikimar da Qurani bai fito karara ya fadi lokacin bude-baki ba. Sannan akwai yankunan da, idan kana dada nisa daga doron Duniya na Arewa ka na tahowa kudu, sai ka sami sassan da Rana ke awa 18 ko 20 ba ta fadi ba, ko kuma wani lokacin hasken Rana ba ya wuce awanni 3-4.
Daɗin daɗawa, yanzu ƴan sama jannati da ke tashar sararin samaniya (International Space Station) ko shekara nawa za su yi a can Rana ba ta fitowa ballantana faduwa. Jiddin ta na nan a sama kiri.
Amfanin ijtihadi ke nan a al’ummar musulmi, domin Allah ya riga ya sanar da mu cewa
Q6:38 “…Ba mu yi sakacin barin komai ba a cikin littafi”
Ayar da babu wanda ya yi mata cikakkiyar fassara irin Sayyidna Umar lokacin da wani ya tambaye shi ya nuna masa yadda ake gurasa a cikin Qurani, sai ya sa aka nemo wadda ta iya yin gurasar domin ta nuna masa. Dogaro da ayar da ta ce fas’alu Ahlul zikri. Wannan ce hanya ta ijtihadi da malamai za su rika zakulo ma’anoni game da abinda ya bayyana ko ya buya.
A taƙaice, wanda ya sha ruwa bayan faduwar Rana kafin duhun dare ya shiga, da wanda ya ce sai bayan duhu ya bayyana, dukkansu na da hujja mai ƙarfi, kuma azuminsu daidai ne. Wajibi Malamai su rungumi tadabburi da tafakkuri kamar yadda Allah Ya yi ta jan hankalinmu a Kur’ani fiye da duk wata ibada. Domin ta haka ne kaɗai, za mu gane ma’anar Annabi a fadarsa cewa “Deen, An nasihat”
Allah ya ganar da mu baki daya.
A sha ruwa lafiya!