Yawan jarin kai tsaye da bai shafi kuɗi ba da ƙasar Sin ta zuba ya ƙaru da kashi 6.3 a rubu’i na farko

Daga CMG HAUSA

Wasu alkaluma da ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin ta fitar jiya Alhamis sun nuna cewa, jarin kai tsaye da ƙasar ta zuba wanda bai shafi harkokin kuɗi ba, ya kai kuɗin Sin yuan biliyan 170.95 a watannin ukun farko na shekara, ƙaruwar kaso 6.3 bisa dari kan na shekarar bara.

Inda aka juya zuwa dalar Amurka kuwa, jarin na ODI ya ƙaru da kashi 8.5 daga shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan 26.92.

A cikin rubu’i na farko, jarin kai tsaye da bai shafi harkokin kuɗi ba da ƙasar Sin ta zuba a cikin ƙasashen da ke kan hanyar shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya, ya ƙaru da kashi 19 cikin ɗari bisa na shekarar bara zuwa dala biliyan 5.26.

Ma’aikatar ta ƙara da cewa, jarin na ODI da aka zuba a ɓangaren manyan hajoji da kayayyaki da ake sayarwa, ya ƙaru da kashi 36.3 bisa ɗari a shekarar da ta gabata zuwa dala biliyan 5.45, yayin da jarin da aka zuba a fannin masana’antu, ya ƙaru da kashi 13.3 cikin ɗari.

Fassarawa: Ibrahim Yaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *