Yawan jarin wajen da aka zuba a ƙasar Sin ya ƙaru da kaso 11.6 a Janairu

Daga CRI HAUSA

Ƙididdigar da ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar Sin ta fitar ya yi nuni da cewa, a watan Janairun shekarar 2022, yawan jarin waje da aka zuba a ƙasar Sin ya kai kuɗin Sin yuan biliyan 102.28 kwatankwacin Dalar Amurka biliyan 15.84, adadin da ya ƙaru da kashi 11.6 bisa na makamancin lokacin bara. Idan kuma an yi nazari, za a gane cewa, jarin da ƙasashen da suka amsa shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya da ma ƙasashen ƙungiyar ASEAN suka zuba ya ƙaru da kimanin kashi 30 cikin ɗari.

A game da wannan, Mista Zhang Jianping, darektan cibiyar nazarin haɗin gwiwar tattalin arzikin shiyya-shiyya ƙarƙashin kwalejin nazari na ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar Sin ya yi nuni da cewa, jarin waje da ake zubawa a ƙasar Sin na ci gaba da ƙaruwa yadda ya kamata bayan jarin da aka zuba a ƙasar ya zarce kuɗin Sin yuan triliyan guda a bara.

Yaya mai cewa,“Kaso 11 cikin ɗari ba ƙaramar ƙaruwa ba ce, wanda ya shaida cewa, a yayin ƙoƙarin neman farfaɗowar tattalin arzikin duniya, duk da matsalolin da ake fuskanta, ƙasar Sin na ƙara janyo jari daga ƙasashen ƙetare sakamakon yadda tattalin arzikin ƙasar ke gudana yadda ya kamata da ma dokar zuba jari ta baki ‘yan kasuwa da yankin gwajin ciniki maras shinge da aka kafa a ƙasar da ma yarjejeniyar ciniki mai ‘yanci da aka cimma da kyautatuwar yanayin kasuwanci na ƙasar da girman kasuwarta da sauransu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *