Yawan mace-macen aure: Rashin haƙuri ko rashin tarbiyya?

Yawan mutuwar aure, matsala ce da ta zama ruwan dare a ƙasar Hausa. Alal misali, bincike na baya-baya da aka gudanar a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya ya nuna cewa rabin auren da ake yi na ƙarewa da saki.

Shin ko me ke janyo wannan matsala? Wane irin tasirin ta ke yi a kan zamantakewar al’umma? Me ya kamata a yi don a rage matsalar?

An yi kira ga gwamnati ta sanya darasin ilimin aure a cikin manhajar karatun sakandare da nufin rage yawan mace-macen aure a cikin al’umma.

Mace-macen aure matsala ne da ya yawaita a ƙasar Hausa. An yi ittifakin cewa jihar Kaduna na da yawan zawarawa manya da ƙananan yara.

Ga wasu daga cikin abubuwan da ake ganin suna haifar da matsalar:

1. Jahilci: Matsala ta farko da take jawo macen aure a ƙasar hausa a wannan zamani itace jahilci da yawan mutanenmu, musamman mutanen, mun jahilci mene ne aure, ma’anarsa da kuma a Addinance. Da yawan matasa da suke aure a yanzu yawancin su basu san ma’anar aure ba, basu san ƙa’idojin aure ba, basu san hukunce-hukuncen aure ba, kai wallahi wasu ma basu san ya ake yin wankan Janaba ba, amma a haka suke zuwa neman aure kuma a basu.

2. Kwaɗayi: Hausawa dai suna cewa, “idan har da kwaɗayi, to da wulaƙanci”, kuma kowa ya hau motar kwaɗayi to zai sauka a tashar wulaƙanci. sannan ƙuda wurin kwaɗayi yake mutuwa. Da yawan mace-macen auren da ke faruwa a ƙasar Hausa suna biyo bayan kwaɗayi ne da a’auratan suke sawa a cikin kwanciyarsu tun kafin su yi aure.

3. Auren dole na daga cikin wuraren da ke kawo yawan mace-macen aure musamman a ƙasar Hausa inda abin ya zamo ruwan dare.

4. Auren Zumunci idan ya yi kyau ya fi komai daɗi, idan kuma ya ɓaci ya fi komai muni. Irin wannan aure kan yi ƙarko ne kawai idan ma’auratan ne suka haɗa kansu.

5. Auren Sha’awa: Auren sha’awa dai shi ne mutum ya yi aure domin kyawun jiki ko surar ɗan uwansa, illar irin wannan auren shi ne; da zarar waɗannan suffofi da aka yi auren domin su suka gushe, to shikenan matsala za ta fara afkuwa a auren, daga nan sai rabuwa.

Wasiƙa daga MALAM SA’ID. 09070905293.