’Ya’ya na kowa ne, a daina cin zarafin ’ya’yan riƙo

Assalam alaikum. Ina miƙa saƙon gaisuwa da ban bajiya ga dukka ma’aikatan jaridar Blueprint Manhaja, Allah Ya albarkaci wannan jarida, Amin.

Wata babbar matsala na tasowa da ta shafi yadda wasu mutane ke ɗaukar ‘ya’yan da ba nasu ba na cikinsu, a wulaƙance, musamman ma dai ‘ya’yan riƙo da suke ɗauko su daga ƙauye ko gidajen ‘yan uwa, don su taimaka musu, ko kuma marayu ne da iyayen su suka rasu. Akwai kuma batun yaran aiki da ake ɗauko su daga ƙauye ko daga gaban iyayen su, don su yi aiki a gidajen masu kuɗi ko ma’aikata, don su taya su aikin kula da gida da yara, a lokacin da masu gida ba sa nan.

Na sani ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, akwai mutanen da suke ɗaukar yaran da ba nasu ba su riƙe tare da yaran cikin su har ka kasa bambanta wanne ne ainihin yaran gidan, ana kula da haƙƙin kowa, kuma ana ba su tarbiyyar da ta dace.

Ko da ‘yan aiki suka ɗauka za ka ga suna tattalinsu, har ma su saka su a makaranta, kuma suna biyansu haƙƙoƙin su a kan lokaci. Sai dai ba su ne akasari suka fi yawa a cikin al’umma ba, don dama ba a taru an zama ɗaya ba.

Sai dai rubutuna na yau a kan waɗancan mugayen masu zaluntar yaran ’yan uwansu ko yaran aikinsu, ba tare da tausayawa ko tunanin abin da suke yi bai dace ba.

Wasu kar ma a je da nisa, ana maganar yaran ‘yan uwa daga ƙauye ko gidajen ‘yan uwa, akwai masu zaluntar ‘ya’yan kishiyoyi da aka mutu ko uwar ta fita ta barsu a tsakar gida, wulaƙanci iri-iri da tozartawa babu wanda ba a nuna musu. Duk dai don ta tabbatar musu cewa su ba ‘yan gata ba ne ko kuma ba ‘yan gida ne.

Masu irin wannan halin, suna nuna wa ‘ya’yansu na cikin su kulawa da soyayya matuƙa, har ma ba sa ganin laifin su a inda suka yi ba daidai ba, a kan masu yi musu aiki ko sauran yaran gida da ba a gidan aka haife su ba.

Wani lokaci ma yaran gida kan yi wa ’yar aiki fyaɗe ko wani nau’i ba cin zarafi, amma sai a ɓoye a tsorata yarinyar da uwar ta don kar a fallasa. Kai har ma da zargin ’yar aikin ko ’yar riƙon kan ita ce ta ƙulla makircin.

Kwanakin baya wani abin takaici ya faru da wata yarinya ’yar shekaru goma sha ɗaya da aka rabo ta daga gaban iyayen ta tun daga Jihar Kebbi zuwa Jos, don ta yi wa wata ma’aikaciya da ke aiki a wata babbar ma’aikata, aikin kula da gida.

Amma sai ta riqa ƙuntata mata, duka da mugunta, har da zaunar da ita a tafasasshen ruwan zafi, ko da yake daga bisani mijin matar ya ce faɗuwa ta yi a cikin ruwan zafin. Amma sakamakon haka yarinyar ta shiga wani mawuyacin hali, har ma kuma kawo lokacin haɗa wannan rubutun ta rasa ranta. Ita kuma matar tana tsare a wajen hukuma.

Wasu matan sam ba su iya kula da ɗan wani ba. Suna ganin kamar ‘ya’yansu ne kawai abin nunawa so da ƙauna. Sauran yara kuma banza. Haka wani lokaci a can baya aka rawaito cewa, wata mata a Jihar Adamawa ta ƙona jikin wata ƙaramar yarinya da ta ke yi wa aiki, ta hanyar manna mata dutsen guga a jiki. Don kawai ta yi kuskure ga wajen wani aiki da aka ba ta. Wannan wacce irin mugunta ce haka da mata suke nunawa yara mata ƙanana da ke taimaka musu a gida.

Wannan mugun hali da mata suke nuna wa yana tauye wa yarinya haƙƙinta, walwalar ta da rayuwarta, kuma suna gadarwa ‘ya’yansu wata irin rayuwa da ba su san yadda za ta kasance da su ba. Su ma wani dalili ya yi sanadin shigarsu wani mugun hannu da za a cutar musu da rayuwarsu.

Rahotanni na nuni da cewa, ɗaruruwan yara ‘yan aikatau ne a Nijeriya, suke fuskantar uƙuba kala kala a hannun iyayen gidan su, inda suke azabtar da su da bautar da rayuwar su, a kan ɗan abin da bai kai ya kawo ba.

Wasu yaran ma ana sa su cikin rayuwar da ba ta dace ba, amma saboda ba a bari a na kai ƙara wajen ’yan sanda ko jami’an tsaro haka labarin ke shirirancewa babu matakin da ake ɗauka. Duk da dokar kare haƙƙoƙin yara da wasu jihohin Nijeriya suka sanya wa hannu, har yanzu hukunta irin waɗannan iyayen riƙo yana wahala.

Ya kamata iyaye su gane haɗarin da suke jefa rayuwar ‘ya’yansu cikin wani mawuyacin hali, ta hanyar tura su aikatau wajen mutanen da ba su ma san su waɗanne iri ba ne. Yaya tarbiyyarsu ta ke, kuma yaya tausayi da kulawar su kan amanar da za su ba su. Mu sani fa yaran nan amana ce a wajen mu, kuma wajibi mu ne mu dage mu yi abin da ya dace. Kada mu riƙa kai su inda kima da mutuncin su za su tozarta.

Allah Ya Sa mu dace, Amin.

Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA, 08168716583.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *