Yayin da watan Azumi ya ƙarato

A makon da za mu ne ake sa ran ɗaukar azumin watan Ramadan, wata mai alfarma ga dukkan Musulmin duniya. A ranakun wannan wata, waxanda suke kamawa guda 29 ko 30 a kowacce shekara, Musulmi sukan kaxaita daga aikata wasu muhimman abubuwa a rayuwar ɗan adam da rana, kamar ci, sha da jima’i. Lokacin haramcin hakan yana kamawa ne daga ketowar alfijir zuwa faɗuwar rana a kulliyaumin.

To, a zahirin gaskiya ba waɗannan abubuwa ne kaɗai abubuwan da ake sa ran Musulmi ya guje su ba, illa dai kawai za a iya cewa, waɗannan abubuwa guda uku, wato ci, sha da jima’i, sun kasance wani ma’auni da zai zama abin gwaji ga halayya da ɗabi’un ɗan adam ta fuskar nuna juriya, dauriya, haƙuri da kuma yakana.


Abin nufi a nan shine, muddin mutum zai iya kauce idanunsa daga ci, sha da kuma saduwa, to ana sa ran zai iya kauce wa dukkan wani abu zuciyarsa za ta iya raya masa cewa, tana buƙatar sa, domin ba kasafai ɗan adam ke cin karo da abinda ya zarce buƙatar waɗancan abubuwa uku ba. To, idan har zai iya barin su, duk da cewa, ana kallon su tamkar tilashi, to lallai kenan zai iya barin wani abu savanin hakan kenan.

A taƙaice dai, idan har mutum zai iya ƙaurace wa ci, sha da saduwar aure, to kenan zai iya kauce wa ɗabi’a ta ƙeta, gulma, cin hanci da rashawa, cin amana, ƙazafi, ƙarya, sata, fashi, ta’addanci da dukkan wani abin ƙi da ake ji ko gani. Don haka, duba da wannan, haƙiƙa za a iya cewa, akwai matuqar ɗimbin hikima a sha’anin umarnin da aka bayar ga Musulmi na ibadar watan Azumi na Ramadana.

Muhimmin abinda ya kamata ɗan adam ya lura da shi kan wannan hikima ta Allah (SWT) na umartar bayinsa da su azumci watan Ramadan shi ne, ashe za su iya kauce wa dukkan wani abu da yake na ƙi ba tare da sun rasa komai a rayuwarsu ba.

A taƙaice ma dai, guje wa abin ƙi, fa’ida ce da shi, domin ga abbubuwan da ba na ƙi ba ne ba ma, amma sun zamo wasu abubuwa masu alheri. Wato ƙaurace wa ci, sha da jima’i ya koyar da kai wani abu mai amfani a rayuwarka ta fuskar ɗabi’a. Bugu da ƙari, hatta likitoci sun tabbatar da cewa, azumi yana inganta lafiyar jikin ɗan adam.

Tabbas da mutane a jimlace za su yi aiki da hikimar da ke cikin azumtar watan Ramadan, da rayuwa ta yi sauƙaƙa. Hatta cin hanci da rashawa da ake ganin sun yi katutu a ma’aikatun gwamnati za su iya zama tarihi. Hatta cin amana da ake ganin sun yi katutu a tsakanin jama’a, za su iya zama abubuwan tunawa kawai watarana. Hatta matsalolin auratayya da ake ganin su ma sun yi katutu a cikin al’umma za su iya wucewa.

Don haka ba hana ka cin abinci ko shan abin sha ko kusantar mata ne kaɗai abin la’akari a lokacin wannan wata mai alfarma ne abin dubawa kaxai ba, a’a, yana da kyau a fahimci hikimar da ke ciki, sahihiyar hikima kuwa. Fa’idar da ke cikin wannan kuwa za ta iya haɗa wa har ga wanda ma ba Muslmin ba ne, domin ita nagarta kowa yana iya aikata ta, imani kuma wani abu ne daban.

Bugu da ƙari, kasancewar malamai sun tabbatar mana da cewa, a cikin watan Azumin Ramadana akwai wata sa’a ta amsa addu’o’in bayi da Allah (SWT) Ya kaɗaice, Ya ware ta gare su, don amsa dukkan abinda suka roƙe shi, to yana da matuqar muhimmanci al’ummar Musulmi su sanya ƙasarsu a cikin addu’o’insu, saboda halin da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki na matsalolin da suka dabaibaye ta.

Haka nan su ma shugabanni, waɗanda Allah Ya ɗora wa alhakin tafiyar da ragamar mulkin ƙasar, suna buƙatar a sanya su a cikin addu’o’i. Kada mu manta da cewa, nagartar shugaba ita ce, kyautata rayuwar waɗanda ya ke shugabanta. Saboda mu na buqatar mu sanya a cikin addu’o’inmu, domin su samu damar kyautatawa da inganta rayuwarmu.

Mu na roƙon Allah Ya amsa ibadarmu kuma ya ji roƙonmu. Allah ya sa wannan wata mai alfarma ya zamo silar shiryarmu da fitar da mu daga cikin dukkan wani ƙunci da ke damun mu bakixaya. Amin summa amin!