Yobe ta Arewa: Kotu ta tabbatar da takarar Sanata Lawan

Daga BASHIR ISAH

Kotun Ƙoli ta tabbatar da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, a matsayin ɗan takarar sanata na Jam’iyyar (APC) a shiyyar Yobe ta Arewa a zaɓen 2023.

Kotun ta tabbatar da nasarar Lawan ne a zaman shari’a da ta yi ranar Litinin.

Idan ba a manta ba, Lawan ya shigar da ƙara Kotun Ƙolin ne domin ƙalubalantar hukuncin Kotun Tarayya mai zamanta a Damaturu, bayan da kotun a Satumban 2022 ta tabbatar da Bashir Machina a matsayin halastaccen ɗan takrar sanata na yankin.

Sau biyu Ahmad Lawan na shan kaye a kotu bayan da ya nemi ƙalubalantar nasarar da Machina ya samu.

Idan za a iya tunawa, Lawan ya yi hari kujerar Shugaban Ƙasa ne inda ya shiga zaɓen fidda gwanin da APC ta gudanar wanda Bola Tinubu ya lashe, yayin da Machina ya lashe zaɓen fidda gwanin takarar sanata a Yobe ta Arewa na APC.