Yulin 2022 zaɓen gwamna zai gudana a Osun – INEC

Daga WAKILINMU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ya zuwa 16 ga Yulin 2022 za a gudanar da zaɓen gwamnan na jihar Osun.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da INEC ta fitar ta hannun sakatariyarta, Rose Oriarian-Anthony a Talatar da ta gabata.

Jadawalin zaɓen mai ɗauke da kwanan wata Yuni 10, 2021, ya nuna tsare-tsaren ayyukan zaɓen wanda za a soma gudanarwa daga 1 ga Fabrairun 2022.