Yunƙurin juyin mulki: Fadar Shugaban Ƙasar Nijar ta yi ƙarin haske

Fadar Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Nijar ta fitar da sanarwa dangane da halin da ake ciki na fargabar yiwuwar shirin juyin mulki a ƙasar inda ta tabbatar da cewa lallai an samu wasu sojoji da ke tsaron fadar shugaban ƙasar da suka ɗauki matakin da ya saɓa wa doka.

A cewar sanarwar, sojojin da suka yi wannan yunƙuri ba su samu haɗin kan takwarorinsu da ke tsaron fadar ba, kuma a halin da ake ciki Shugaba Bazoum Mohamed da iyalinsa na cikin ƙoshin lafiya.

Rundunar sojin Nijar ta ce a shirye take ta ɗauki matakin murƙushe dukkanin waɗanda suke da hannu a yunƙurin saɓa wa dokar da aka yi a baya-bayan nan, muddin ba su gaggauta tuba ba.

Da safiyar ranar Laraba jami’an tsaron da lamarin ya shafa suka ɗauki matakin datse hanyar da ke kaiwa Fadar Shugaban Ƙasar a cikin wani yanayi da ake fargabar mai yiwuwa na barazanar juyin mulki ne.