Yunƙurin siyasantar da sha’anin wasanni ba zai taɓa yin nasara ba

Daga SAMINU HASSAN

Kafin buɗe gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta birnin Beijing dake gudana yanzu haka, gwamnatin Amurka ta shafe tsawon lokaci tana yi wa Sin matsin lamba, tare da ƙoƙarin amfani da lokacin gudanar gasar ta Olympics, a matsayin wani makami na siyasa, don sarrafa akalar ƙawayenta su juya wa ƙasar Sin baya, inda Amurka ta sha fakewa da batun kare haƙƙin bil adama, a yunƙurinta na cimma wannan mummunar manufa.

Bisa hakan ne ma, ’yan siyasar Amurka suka ayyana ƙaurace wa gasar ta birnin Beijing, a matsayin wani mataki na matsin lambar diflomasiyya. To sai dai kuma, rashin halartar jami’an na Amurka bai haifar da wani koma baya ga wannan ƙasaitacciyar gasa ba, maimakon haka ma, gasar ta yi matuƙar karɓuwa ne tsakanin ’yan kallo na ƙasa da ƙasa.

Bisa ci gaba da ake samu ta fuskar amfani da kafofin sada zumunta, da sabbin kafofin watsa shirye-shirye ta yanar gizo, gasar Olympics ta Beijing ta shekarar 2022, ta zamo wadda aka fi kallo a tarihin ta, inda a Amurka ma, adadin masu kallon ta suka zarce waɗanda aka taɓa gani a baya.

Masharhanta da dama na ganin cewa, bunƙasar abota tsakanin ’yan wasan motsa jiki na Sin da Amurka da aka gani, a yayin da wannan gasa ta lokacin hunturu, ya kawar da tasirin da ’yan siyasar Amurka ke fatan ƙauracewar tasu za ta haifar.

An ga yadda ’yan wasa da yawa daga Amurka suka riƙa yayata kyakkyawan yanayin wannan gasa a kan shafukansu na sada zumunta. A hannu guda kuma, adadin Amurkawa da suka kalli wannan gasa ta Olympics ta birnin Beijing ta kafar NBC Universal dake Amurka, ya kai sama da mutum miliyan 100, wato kimanin mintunan watsa shirye-shirye biliyan 2.23 ke nan. Hakan dai ya isar da wani saƙo mai ƙarfi, cewa duniya za ta ci gaba da jura yunƙurin masu siyasantar da al’amuran da ba na siyasa ba, domin cimma burin kashin kai.

Ko shakka babu, kawance, da abota da wasanni ke ƙullawa ya wuce batun kan iyakokin ƙasashe, kuma zai yi wuya a yi amfani da harkar wasanni wajen cimma wani ƙuduri na siyasa, saɓanin tunanin da ’yan siyasar Amurka suka yi tun da farko.