Yunƙurin tsige Buhari ɓata wa kanku lokaci ne – Garba Shehu ga sanatoci

Daga AISHA ASAS 

Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya ta maida martani ga sanatocin jam’iyyar hamayya ta PDP da suke yi wa Shugaba Muhammadu Buhari barazanar tumɓuke shi. 

Blueprint ta ce, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu ya fitar da wani jawabi a ranar Alhamis a matsayin martani. 

Garba Shehu ya kuma yabi shugaban majalisar dattawa wanda ya takawa sanatocin burki, inda Garba Shehu ya bayyana cewa, Ahmad Lawan ya yi abin da ya kamata. 

A jawabin da ya fitar, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya ce, sanatocin PDP da suka fice daga majalisa saboda maganar, sun nuna halin yarinta, kuma suna ma vata wa kansu lokaci ne. 

Garba Shehu ya ƙara da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari tana namijin ƙoƙari ne wajen yaƙi da ‘yan ta’adda tare da shawo kan matsalar tsaro, har da wanda ta gada daga hannun gwamnatin PDP. 

“Muna maraba da haɗin kansu wajen ƙoƙarin magance matsalolin da mutanen Nijeriya ke fuskanta kullum. 

“Babu wanda ya nemi su yi yunƙurin tsige shugaban ƙasar da aka zaɓa, yana shirin kammala wa’adin ƙarshe.” 

Shehu yana ganin ‘yan majalisar dattawan sun ɗauko dala babu gammo, domin ba waɗanda suke wakilta suka nemi a sauke Buhari ba. 

“Sai su tambayi kansu, suna son aiki a gwamnati ne ko kuwa suna son shiga labarai ne? Idan aiki za su yi, sai su dage, su daina raina masu zaɓe a Nijeriya. 

“A maimakon hakan, su yi koyi da Amurka, inda ‘yan adawa ke ɓata lokaci a tattauna muhimman batutuwa kamar tsadar rayuwar da ake fuskanta a duniya,” a cewar Garba Shehu.