Yunƙurin tsige Shugaba Buhari abin takaici ne – Adamu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya bayyana yunƙurin tsige Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da wasu ‘yan majalisun tarayya suka yi da wani lamari abun takaici ne.

Adamu ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da kafar talabijin ta Trust TV ranar Talata, 9 ga watan Agusta, 2022 a birnin tarayya Abuja.

Idan ba ku mance ba Manhaja ta kawo muku rahoton cewa ‘yan majalisun tarayya sun yi barazanar fara bin matakan tsige Shugaban ƙasa daga kujerarsa a wani taron manema labarai jim kaɗan kafin tafiyar su hutun watanni biyu.

Mambobin majalisar sun yanke wannan hukuncin ne bayan sun bai wa shugaban ƙasar wa’adin makonni shida ya shawo kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasar nan.

Da yake maida martani kan batun, Shugaban APC na Ƙasa kuma tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu ya ce yunƙurin babban abin takaici ne, “wanda ya bar kan turba mai kyau.’

A kalamansa ya ce: “Shirin shige Shugaban Ƙasa babban abin takaici ne da babu shi kwata-kwata yanzu. Tare da majalisar tarayya, muna tsammanin irin haka, yana faruwa a ko’ina a kowace dimokuraɗiyya.

“A duk lokacin da ya zo kanka, ka cigaba da ƙoƙari, hatta waɗanda suka ƙirƙiri yunƙurin sun sauya daga kan hanyar.”

Da yake martani kan yajin aikin Malaman Jami’o’i da ƙoƙarin jam’iyya mai mulki ke yi na ganin ɗalibai sun koma azuzuwansu, Adamu ya ce APC ta yaba ƙwarai da yadda iyaye da ɗalibai ke nuna damuwar su.

Ya kuma yi fatan cewa Ƙungiyar ASUU za ta “dawo cikin hayyacinta a zahirance” ta dawo kan teburin sulhu.

“Ban sani ba kuma Ina yaba wa da namijin ƙoƙarin da gwamnati ke yi, kana ina fatan ASUU za ta dawo hayyacinta tare da gwamnati, ta haka kaɗai za mu cimma matsaya.”