Daga Umar Garba a Katsina
Matar nan mai suna Ai’sha Abubakar da jami’an tsaro suka cafke ɗauke da tarin harsashin bindiga ta ce yunwa ce ta jefa ta harkar yi wa ‘yan bindiga safarar harsasai.
A ƙarshen makon da ya gabata Blueprint Manhaja ta rawaito cewar jami’an tsaron dake sintiri a kan hanyar Abuja sun kama wata mata da ta hau motar sufuri ta jihar Katsina wato KTSTA daga jihar Nassarawa zuwa jihar Katsina.
An kama ta ne ɗauke da harsashin bindiga da ba a ƙididdiƙe yawansa ba cikin buhu a ƙoƙarinta na kai wa ‘yan bindigar dake ta’addanci a jihar Katsina.
Da farko Aisha ta musanta aikata safarar harsashin, a cewarta wani mutum ne ya ba ta shi a cikin buhu ba tare da ta san ko meye a ciki ba.
“Ban san ko meye a ciki ba,wani mutum ne ya bani, ban san mutumin ba kuma ban san sunan shi ba, ban san inda yake zaune ba.” Inji ta.
To sai dai daga baya Ai’sha ta amsa zargin da ake mata inda ta shaida wa jami’an tsaro cewa yunwa ce ta tilasta mata shiga harkar.
“Ban taɓa aikata irin wannan laifin ba a baya, yunwa ce ta tilasta min na shiga”. Inji Ai’sha.
Da aka tambaye ta ina za ta kai alburusan sai ta ce, an bata umarni ne ta ajiye shi a bakin Rafin Hayin ‘Yan tumaki dake ƙaramar hukumar Ɗanmusa daga baya wani mutum zai zo wurin ya ɗauka buhun.
Zagalo Makama dake sharhi kan harkar tsaro ya yi tsokaci kan lamarin, a shafinsa na X ya bayyana cewa kama Ai’sha Abubakar wani cigaba ne da aka samu a ƙoƙarin da jami’an tsaro ke yi don daƙile yaɗuwar haramtattun makamai.