Yunwa ta sa yaro ya faɗi ana tsaka da shari’ar zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO A. BABAJI

A safiyar ranar Juma’a ne wani abu mai kama da wasan kwaikwayo ya faru a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja bayan da wani matashi daga cikin matasa masu zanga-zanga da aka tsare ya yanki jiki ya faɗi gabannin fara shari’a.

Matashin, ɗaya ne daga ciki masu ƙananan shekaru da ƴan sanda suka kama a lokacin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a watan Agusta.

Wasu hotuna da bidiyo sun nuna yadda aka ga wasu daga cikin matasan sun gaggauta kai ɗauki wa yaron inda kuma wani hoton ya nuna wani Alƙali na ƙoƙarin taimakon sa.

Bayan wani hukunci da Mai Shari’a Nwite Emeka ya yi ne a baya, ƴan sanda suka tsare matasan har na tsawon kwanaki 60 don ba su damar kammala bincike akan su na zargin haddasa tashin-tashina a wasu sassan Nijeriya.