Zaɓaɓɓen Gwamnan Jigawa ya karɓi shaidar lashe zaɓe, ya nemi haɗin kan al’ummar jihar

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi Ɗan Modi, ya nemi haɗin kan al’ummar jihar Jigawa a lokacin da yake karɓan shedar lashe zaɓe daga hukumar INEC.

Gwamnan Umar Namadi wanda ya bayyana haka a Hedkwatar hukumar INEC ta ƙasa da ke Dutse, ya ce a shirye yake domin sauke dukkanin alƙawuran da ya ɗauka lokacin gudanar da kamfe ɗinsa amma dole sai al’ummar jihar sun ba shi haɗin kai da goyon baya.

Da yake jawabi Baturen Zaɓe na Jihar Jigawa, Farfesa Muhammad Lawan Bashir ya hori sabin shugabannin da su zama sun sauke nauyin al’umma da ya rataya a kansu.

Sabon Gwamnan da ‘yan majalisun jiha 27 a cikin 30 sun karɓi shaidar lashe zaɓen bayan da ƙananan hukumomin Dutse, Birnin Kudu da ‘Yan Kwashi INEC ta bayyana zaɓensu wanda bai kammalu ba wanda dole sai an sake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *