Gwamna mai jiran gado a Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa kwamiti mai mutane 60 a yayin da yake shirin karɓar mulkin ji har.
Ofishin zaɓaɓɓen gwamnan ne ya bayyana hakan, a wata sanarwa da Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a ranar Laraba, inda ta bayyana cewa Kwamitin yana da alhakin tuntuɓar gwamnatin Gwamna Bello Matawalle mai barin gado, gabanin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu a jihar.
Tsohon Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, MD Abubakar CFR ne zai jagoranci kwamitin, a yayin da Dr. Hamza Mohammed zai zama Sakatare.
Har ila yau, Kwamitin ya haɗa da tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar Zamfara, Mujitaba Isah Gusau; Kanal Bala Mande (mai ritaya); Farfesa Abubakar Aliyu Liman; Barista Nura Ibrahim Zarumi; Barista Bello Galadi da sauransu.
Kwamitin dai ya ƙunshi masu fasaha, masu riƙe da muƙaman gwamnati da masu ritaya da kuma ƙwararru da masana daga kowane ɓangare na rayuwa.
Babban aikin Kwamitin shi ne samar da tsarin tuntuɓar juna tare da kafa hanyar sadarwa ta yau da kullum tare da gwamnati mai barin gado domin karɓar mulki cikin nasara.
Bugu da ƙari, kwamitin zai tuntuɓi ma’aikatu, sassa da hukumomi (MDAs) tare da duba kudaden gwamnati mai barin gado tare da mai da hankali kan rasit, kadarori da lamuni da sauransu.
Nan gaba kaɗan ne za a bayyana ranar da za a ƙaddamar da Kwamitin Karɓar Mulkin na Gwamna.