Zaɓar Asma’u Inuwa a matsayin Shugabar Matan Gwamnonin Arewa sara ne kan gaɓa – Esther Amisu

Daga ABUBAKAR A. BOLARI a Gombe

Esther Amisu, ‘yar siyasa ce a jihar Gombe kuma ƙwararriya a ɓangaren sanin harkokin siyasa, ta ce ba shakka matan Gwamnonin Arewa ba su yi zaɓen tumun dare ba na zaɓar Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa Yahaya, uwargidan gwamnan Gombe a matsayin jagora.

Esther Amisu, ta ce zaɓar Asma’u Inuwa Yahaya da matan gwamnonin suka yi zai ƙara bai wa mata dama na shiga harkokin siyasa domin Asma’u mace ce da a kullum take ƙoƙarin mata sun samu kulawa ta musamman an kuma basu wani kaso mai tsoka a muqaman siyasa.

Ta yi wannan batu ne a wani taron manema labarai da ta kira a Gombe inda ta yi amfani da damar ta taya uwargidan gwamnan na Gombe Asma’u murna na zaɓenta da matan gwamnonin Arewa suka yi ta zama shugabar su.

Esther Amisu, gogaggiyar ‘yar siyasa ce wacce da ita aka kafa Jam’iyyar CPC har ta haɗe aka yi maja da wasu jam’iyyu ta zama Jam’iyyar APC ake damawa da ita ba tare da ta taba canja sheqa zuwa wata jam’iyya ba.

A cewar ta Ƙungiyar Matan Gwamnonin Arewa sun yi sa’ar shugaba domin Hajiya Asma’u Muhammad Inuwa Yahaya, shugaba ce adala mai son ganin ta taimaki al”umma musamman ma masu ƙaramin ƙarfi wanda hakan ya sa ta kafa gidauniyar ta mai suna Jewel Care Foundation da take ɗaukar nauyin jinyar mabuƙata.

Har ila yau Esther ta ƙara da cewa Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, Yar siyasa ce da take da ɗimbim magoya baya a tafiyar siyasa tun kafin maigidanta ya zama gwamna kuma hakan zai sa ta sake samun goyon bayan sa wajen ƙara jan wasu matan su shiga siyasa ana damawa da su.

Amisu, tana da tabbacin idan Asma’u Inuwa Yahaya, ta zauna da mijinta ta karanta masa wasu hanyoyin ci gaban Nijeriya da matan Nijeriya zai ƙara mata ƙwarin guiwar tafiyar da shugabancinta.

Daga nan sai ta bai wa Shugabar Matan Gwamnonin shawarar cewa ta ja su a jiki wajen karɓar shawarwarin su domin zai ƙara mata hikima wajen tafiyar da shugabancinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *