Zaɓe: EFCC ta cika hannu da mutum 12 a Kano da Katsina kan sayen ƙuri’a

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Rasha da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) ta ce, ta tsare mutum 12 bisa zargin sayen ƙuri’a yayin zaɓen cike givin da ya gudana a Kano da Katsina ranar Asabar.

Shuguban EFCC na shiyyar Kano, Faruk Dogondaji, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) cewa, an kama waɗanda ake zargin da tsabar kuɗi Naira miliyan 1.5 a jihohin Kano da Katsina.

A cewarsa, am damƙe 10 daga cikinsu ne a yankin Ƙaramar Hukumar Doguwa, Jihar Kano, sannan biyu a yankin Ƙaramar Hukumar Kankiya a Jihar Katsina.

Jami’in ya ce an cafke waɗanda lamarin ya shafa ne a daidai lokacin da suke ƙoƙarin sayen ƙuri’a daga masu zaɓe a rumfunan zaɓe.

Ya ce an kama 10 ɗauke da kuɗi miliyan N1,357,500 a Ƙaramar Hukumar Doguwa, biyu kuma ɗauke da N242,000 Kankia, Jihar Katsina.

Ya ƙara da cewa za su gurfanar da waɗanda ake zargin da zarar sun kammala bincike.