Zaɓe: INEC za ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha kafin 2023

Daga WAKILIN MU

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ta na nan ta na sake nazari kan hanyoyin fasaha da ta ke amfani da su a wajen zaɓuɓɓuka, da nufin shigo da waɗansu sababbi waɗanda za su inganta zaɓuɓɓukan da za a yi daga yanzu zuwa shekara ta 2023.

Daraktan Wayar da kan Masu Zaɓe da kuma Sashen Yaɗa Labarai na INEC (VEP), Mista Nick Dazang, shi ne ya bayyana haka a wajen wani taron ƙara wa juna sani na sashen nasu mai taken “Sake Duban Kundin Wayar da kan Masu Zaɓe na Ƙasa” wanda aka yi a garin Keffi, Jihar Nasarawa, a ranar Talata.

Taron, wanda na tsawon kwana biyar ne, INEC tare da haɗin gwiwar wata gidauniya mai suna Westminster Foundation for Democracy (WFD) su ka shirya shi.
 
A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a gefen wajen taron, Dazang ya ce Hukumar Zaɓen ta soma aikin yin zaɓe ta hanyar intanet ne tun a cikin 2004 lokacin da ta shigo da tsarin yin rajista da fom-fom waɗanda aka ɗauka da komfuta.

Ya ce, “Bayan wannan sai a cikin 2010, hukumar ta shigo da tsarin amfani da injinan ɗaukar bayanai kai-tsaye, wanda daga nan kuma ta faɗaɗa tsarin amfani da injinan a wajen gudanar da zaɓen shekarar 2011.

“Saboda haka, mun fara wannan tsarin ne tun a cikin 2004, wanda ya kai mu ga yin amfani da kati mai karanta bayanai a komfuta (Smart Card Reader, SCR) da kuma katittikan zaɓe na dindindin, wato Permanent Voter Cards (PVCs) waɗanda mu ka yi amfani da su a cikin 2015.

“Amma hukumar ta na sake duban fasalin wannan tsarin da nufin ɗaga daraja tare da inganta yadda za a gudanar da zaɓuɓɓukan 2023.

“Hukumar na so ta shigo da sababbin hanyoyin fasaha waɗanda za su taimaka wajen kamɓama zaɓuɓɓuka, sannan su inganta su. Saboda haka dai hukumar na aiki tuƙuru kan wannan.

“Nan ba da jimawa ba, lokacin da hukumar ta gama shawartawa, za ta fito ta bayyana wa ‘yan Nijeriya yadda za a yi wannan ɗin.”

Dazang ya ƙara da cewa a wajen shigo da sababbin hanyoyin fasahar, INEC za ta sake duban yadda ake amfani da injin karanta katin zaɓe kuma ƙila ta shigo da wasu sababbin hanyoyin fasahar waɗanda za su yi aiki sumul ƙalau tare da masu zaɓe ta hanyar intanet a cikin 2023.

“Hukumar ta na yin aiki a kan hakan a tsawon watanni kuma idan Allah ya yarda nan da watanni kaɗan hukumar za ta sanar da jama’a matsayin ta.”

Ya ce INEC za ta ci gaba da shigo da sababbin hanyoyin fasaha cikin tsarin gudanar da zaɓe, ba wai don saboda burgewa ba, sai don hanyoyin fasahar za su amfanar.
 
Ya yi la’akari da cewa hukumar ba ta yi nadamar amfani da hanyoyin fasahar da ta riga ta shigo da su wajen gudanar da zaɓuɓɓuka a Nijeriya ba zuwa yanzu domin sun taimaka gaya wajen inganta tsarin da kuma fayyace gaskiya.

Dazang ya ce hukumar ta na kuma sake kallon tsarin ta na wayar da kan masu zaɓe domin ta samu damu damar yin bayani sosai kan yadda sabbin hanyoyin fasahar ga ‘yan Nijeriya.
 
Ya ƙara da cewa: “A wajen sake fasalin tsarin mu na wayar da kan masu zaɓe, mu na kallon wasu al’amura da su ka haɗa har da sababbin hanyoyin fasaha waɗanda hukumar ta ke da niyyar shigo da su.

“Tilas ne mu san yadda abin ya ke sosai saboda mu san yadda za mu iya yin bayani kan yadda waɗannan kayayyakin fasahar su ke aiki ga ‘yan Nijeriya kamar yadda mu ka yi lokacin da mu ka shigo da tsarin SCR, da injinan ɗaukar bayanai kai-tsaye da kuma PVCs.”

Ya bayyana aikin wayar da kan masu zaɓe a matsayin wani babban ginshiƙi na harkar gudanar da zaɓe wanda ke buƙatar yin aiki kafaɗa da kafaɗa ba kawai daga INEC ba har ma daga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin.
 
Bugu da ƙari, Dazang ya ce, “Idan ka kalli abin da ke faruwa a sauran ƙasashen duniya, har ma da Nijeriya, sauye-sauye da dama su na ta aukuwa waɗanda su ka tilasta lallai a sake duban fasalin yadda ake faɗakar da masu zaɓe.”

A cewar sa, hakan ya haɗa da batun sauye-sauye a ɓangaren hanyoyin fasaha da kuma cutar korona, ya ƙara da cewa akwai buƙatar mu sauya tsarin mu na sadarwa domin mu tafi tare da zamani.
 
Ya ce, “Akwai buƙatar mu sauya tsarin mu na sadarwa saboda ƙaruwar yawan matasa. Akwai buƙatar mu yi amfani da hanyoyin fasaha da za su yi daidai da yawan matasan ƙasar mu da matan ƙasar mu.”

A kan batun garambawul da aka yi wa Dokar Zaɓe, Dazang ya ce hukumar na nan ta na aiki tuƙuru tare da kwamitocin nan biyu da Majalisar Tarayya ta kafa, ya ƙara da cewa an samu babban cigaba a kan garambawul ɗin.

Ya bayyana fatan cewa Majalisar Taraya za ta yi abin da ya dace game da wannan ƙalubalen don cika alƙawarin da ta yi wa ‘yan Nijeriya cewar za ta yi wa Dokar Zaɓe kwaskwarima kafin ƙarshen watanni huɗu na farko na shekarar 2021.
 
A kan batun zaɓen gwamnan Anambra, daraktan ya ce hukumar za ta fito da kwanan wata da jadawalin ranakun gudanar da zaɓen a lokacin da ya dace nan gaba, aƙalla watanni shida kafin zaɓen.

Ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su ƙara wa kan su sani game da sababbin hanyoyin fasaha a ko da yaushe, sannan su ci gaba da bin ƙa’idojin kare kai daga cutar korona.
 
Shi kuma wakilin WFD a Nijeriya, Mista Adebowale Olorunmola, ya bayyana ƙudirin gidauniyar su na ci gaba da jajircewar ta da ba INEC goyon baya domin a zurfafa wayar da kan masu zaɓe a Nijeriya, musamman a yankunan karkara.

Ya ce gidauniyar su ta fara yin haɗin gwiwa da INEC ne tun a cikin 2015 don tabbatar da ƙara shigar mata da naƙasassu cikin harkar gudanar da zaɓe.

Olorunmola ya yabi INEC saboda yadda ta ba wayar da kan masu zaɓe muhimmanci da shigar da mata da naƙasassu cikin harkar zaɓe.

Ya ce wannan taro da aka shirya ya na da muhimmanci wajen inganta wayar da kan masu zaɓe daga yadda ake yi yanzu zuwa yadda za a inganta shi saboda zaɓuɓɓukan da ke tafe.

Ya ce, “Babu abin da ya fi ingantaccen tsarin dimokiraɗiyya a yanzu, sai dai a ci gaba da aiki.
 
“Idan ka kalli abin da ke faruwa a Amurka duk da ɗimbin shekarun da su ka kwashe su na aiwatar da mulkin dimokiraɗiyya har yanzu su na ƙoƙarin inganta hanyoyin faɗakar da masu zaɓen su.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *