Zaɓe: Tarihi ya maimaita  kansa a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Tun lokacin da iskar guguwar siyasa ta soma kaɗawa dai ‘yar manuniya ta nuna tarihi zai maimaita kansa bisa irin cin kashin da aka yi wa jam’iyyar PDP a lokacin mulkin shugaban Goodluck Ebele Jonathan.

Jihar Kebbi ma bisa ga dukkan alamu ta bi sahun waɗansu jihohi inda a kullum safiya ta Allah al’umma sai tururuwa suke yi suna canza sheƙa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP ta adawa.

Alhaji Ibrahim Kunne Gulma wani jigo ne a jam’iyyar APC da babban hadimin tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Alhaji Bilyaminu Bawale Sardaunan matasan Kabi ya karɓa tare da magoya bayansa  ya bayyana dalilin barin jam’iyyar zuwa PDP inda ya ce tun lokacin da ya soma siyasa bai taba ganin irin wannan mulkin na kama-karya ba.

Abinda kowa ya sani ita dai siyasa ba abinda waɗansu ‘yan tsirarru ke shiga ɗaki suna aiwatar da abinda suke so ba ce, a’a aba ce da kowa ke da haƙƙin bayar da irin tasa gudummawa musamman wajen aiwatar da ayyuka don amfanin kowa amma a wannan jihar ta Kebbi ba wani ɗan siyasa da aka taimaka babu wani aiki na a zo a gani duk tsawon shekaru takwas da take mulki. 

Idan za a iya tunawa a kakar zaven shekarar 2015 lokacin da waɗansu jam’iyyoyi da suka haɗa da ANPP da AD da ACN suka haɗu suka haifi APC domin murƙushe jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin ya sami nasara inda Sanata Atiku Bagudu ya tsallako bai fi sati biyu a cikin APC ba kuma ya sami nasarar zama ɗan takarar kujerar gwamna a Kebbi.

Bayan guguwar siyasa ta kai Atiku Bagudu samun nasarar lashe zaɓe bisa ga hasashen samun ingantaccen canji sai abin ya zamo kwamma jiya da yau saboda tun tashin farin a cikin shekarar farko aka soma kai ruwa rana tsakanin gwamna Atiku Bagudu da yayan jam’iyyar APC wanda a sanadiyyar haka jam’iyyar ta vare gida biyu da ya zamo sanadiyyar barin jam’iyyar ga waɗansu jiga-jigan siyasar jihar.

Kafin wannan lokacin dai ‘ya’yan jihar Kebbi tun ma ba ‘yan siyasa ba suka rinƙa tofin Allah tsine sanadiyyar rashin iya shugabanci da kuma mulki irin na son kai na waɗansu ‘yan tsirarru da ba su wuce mutane biyar ba wanda tunanin irin yadda suka yi wa jam’iyyar PDP a baya ya sanya yanzu haka a duk inda tawagar jam’iyyar APC ta shiga wajen yaƙin neman zaɓe a kan yi musu ruwan duwatsu tare da farfasa motoci wani lokacin har da duka.

Wannan ya sanya jikin gwamna Atiku Bagudu ya yi sanyi dangane da takarar kujerar ɗan majaisar dattawa a maimakon haka ya bayar da ƙarfi wajen ganin ɗan takararsa na shugabanci Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai saboda a tunanin sa idan APC ta kafa gwamnati zai iya samun matsayi a gwamnatin tarayya.

Yanzu haka dai sai nuna yatsa ake yi tsakanin gwamna Atiku Bagudu wanda ya dogara ga aringizon ƙuri’a da amfani da jami’an tsaro da ma’aikatan zaɓe  da sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC inda ta kai ga raba hanya tsakanin babban hadiminsa Faruqu Musa Enabo wanda shi ne ya yi uwa da makarɓiya wajen dagula harkokin mulki da siyasar jihar Kebbi da gwamna Bagudu ya sakar masa komai a hannunsa ba tare da la’akari da ƙananan shekarunsa ba.

Kawo yau akwai tsofaffin manyan sakatarori sama da talatin da suka yi mubayi’a da PDP kuma waɗansu sahihan majiyoyi sun tabbatar wa jaridar Blueprint manhaja da cewa akwai yiyuwar waɗansu sama da ashirin da ke kan hanya kafin zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *