Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Gwamnatin Kano ta taƙaita zirga-zirga

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin a Kano a yau, gwamnatin jihar ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga daga ƙarfe 12 na daren ranar Juma’a zuwa ƙarfe 6 na yammacin Asabar don kammala shi cikin lumana.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Baba Halilu Ɗantiye ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan da aka shawarci hukumomin tsaro.

Ana gudanar da zaɓen ne a gundumomi 484 na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar.

An kuma ɗaga kafa ga waɗanda ke ayyuka na musamman su gudanar da harkokinsu a lokacin zaɓen.

Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta jaddada aniyarta na yin zaɓen bisa ga gaskiya da adalci da kuma lumana.