Zaɓen ƙananan hukumomi: Mazauna Kano sun kiyaye dokar taƙaita zirga-zirga

Daga BELLO A. BABAJI

Yayin da ake cigaba da gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi, al’umma a Kano suna ƙoƙarin kiyaye dokar taƙaita zirga-zirga da gwamnatin jihar ta saka don tabbatar da an kammala su cikin lumana.

Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan da Babbar Kotun kasar jihar ta bai wa Hukumar zaɓe ta KANSIEC damar gudanar da zaɓen tare da rushe yunƙurin wasu jam’iyyu na dakatar da shi.

Mai Shari’a, Sanusi Ma’aji wanda shi ya yi hukunci kan batun, ya ce KANSIEC ta na da damar gudanar da zaɓe a baki ɗaya ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Da farko dai, KANSIEC ta gabatar da ƙarar ne akan babbar jam’iyyar adawa ta APC a jihar da wasu jam’iyyu 13, inda Alƙalin ya ce duk wani yunƙuri da zai kawo tsaiko wa zaɓen, abin a yi watsi da shi ne.

Alƙalin ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro su tabbatar da bada kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma a yayin zaɓen.