Zaɓen 2023: Ƙalubalen da ke gaban Tinubu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Yanzu dai ta tabbata, Sanata Bola Ahmed Tinubu, na Jam’iyyar APC shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata, da ƙuri’u Miliyan 8 da dubu 794 da 726. Bayan ya samu kashi 25 a cikin ɗari na yawan ƙuri’un da aka kaɗa daga jihohi 30, tare da da samun mafi rinjaye ƙuri’u a jihohi 12 na tarayyar Nijeriya.

Shi kuma wanda ya zo na biyu shi ne ɗan takarar shugaban qasa a jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa, da ya samu ƙuri’u Miliyan 6 da dubu 984, da 520. Kamar yadda Shugaban Hukumar Zave Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu ya sanar da asubahin ranar Laraba, bayan kammala karɓar rahoton sakamakon zaɓen da aka kaɗa a jihohin Nijeriya 36 har da Babban Birnin Tarayya Abuja, daga shugabannin tattara sakamakon zaɓen da da hukumar ta INEC ta tura don sa ido kan zaɓen a dukkan faɗin ƙasar nan.

Zaɓe dai ya gudana cikin lumana, kusan a mafi akasarin ƙasar nan babu wani rahoto mai ɗaga hankali da ya hana zaɓen, in ban da a wasu wurare ƙalilan da suka haɗa da jihohin Legas, Bayelsa, Imo, Edo, Kogi, da Filato, kamar yadda rahotanni suka nuna. Akwai kuma wani hari da aka ce ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai kan Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. A Jihar Gombe ma an yi zargin cewa jami’an tsaro sun harbe wani ɗan bangar siyasa da ya yi yunƙurin satar akwatin zaɓe, rahoton da har kawo rubuta wannan sharhi ba a tabbatar da ingancinsa ba. Sai dai jaridar ThisDay ta rawaito yadda wasu ‘yan tsagera suka riƙa kai hari da tarwatsa aikin zaɓe a wasu yankunan Jihar Legas. Kodayake rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da tsare wasu da ke da hannu a waɗannan hare hare.

Haka kuma rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa sun far wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa a Jos, yayin da ake tsakiyar tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan Majalisar Ƙasa, inda aka ce sun haifar da tsaiko wajen gabatar da rahoton zaɓen wani yanki daga Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa, wanda ya shafi batun zaven ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Bassa da Jos ta Arewa, zaɓen da ya daɗe yana haifar da ƙalubale ga zaman lafiyar jihar fiye da shekaru 20, saboda mabambantan ra’ayoyi da ƙabilu da ke zaune a yankin.

Wani abu da za a iya cewa ya haifar da fargaba da rudani a wannan Babban Zaɓe shi ne batun haɗin kan wasu ‘yan Nijeriya suka yi game da cewa, ba za su goyi takarar Musulmi da Musulmi ba, saboda Jam’iyyar APC mai mulki ba ta mutunta haƙƙinsu na ‘yan ƙasa ba, wajen ba da muƙamin wanda zai yi takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa ba. Don haka suka yi gayyar ƙwansu da qwarqwatarsu domin mara wa takarar ɗan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi tsohon Gwamnan Jihar Anambra, daga Kudu maso yammacin Nijeriya. Wannan matsaya da suka yi ta sauya akalar siyasar Nijeriya, musamman a wannan zaɓen, inda akasarin ‘yan Nijeriya suka yi zaɓe da sunan addini ba don kishin ƙasa ko cancanta ba.

Wannan shafin ya daɗe yana faɗakar da ‘yan Nijeriya illar shigar da batun ƙabilanci ko addini a cikin sha’anin zaɓe, domin tasirin hakan wajen raba kan jama’a da haifar da fargaba da rashin zaman lafiya. Ko da yake cikin jawabin sa na murnar samun nasara sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci dukkan ‘yan Nijeriya su haɗa lai, tare da bashi goyon bayan da zai taimaka masa wajen sauke nauyin da ya hau kansa, ba tare da nuna wariya ga wani ɓangare na ƙasar nan ba. Amma duk da haka babu tabbacin wannan kira nasa zai samu karɓuwa a wajen wasu ‘yan ƙasa da suke ganin ba shi ya fi cancanta da kujerar ba. Ko kuma suna ganin ba za a yi wa mabiya addininsu ko ɓangaren su adalci ba, saboda abubuwan da suka faru.

Lallai yana da matuƙar muhimmanci ga dukkan ‘yan Nijeriya su yi haƙuri su haɗa kai don ganin sabuwar gwamnati mai zuwa ta samu nasarorin da za su kai ga dawo wa ƙasar nan martabar ta da kimarta. A rungumi juna, a kawar da bambancin da yake daɗa kawo mana rabuwar kai. Mu zauna mu tattauna yadda za a tafiyar da ƙasar nan ta yadda kowanne vangare zai bayar da tasa gudunmawar ga cigaban Nijeriya bakiɗaya.

Sannan ya kamata sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da muƙarrabansa su yi la’akari da wasu muhimman matsaloli da suka addabi ƙasar waɗanda a dalilin wasu daga ciki ne ma talakawa suka zaɓe su, domin kyautata zaton za su yi musu adalci wajen ganin an kawo sauyi da gyara a kansu, domin rayuwar talaka ta inganta. Kyakkyawan misali shi ne batun canjin kuɗi, wanda a dab da Babban Zaɓe gwamnati mai ci ta ɓullo da shi, wanda kuma ya kawo ruɗani a cikin ƙasa. Lallai ya zama daga cikin farkon abin da za a fara ɗaukar mataki a kansa, domin talakan Nijeriya ya shaida an samu canjin gwamnati. A samar da wadatar kuɗi a cikin ƙasa, talakawa su samu walwala da sauqin mu’amala ta kasuwanci da cinikayya a ƙauyuka da birane, musamman ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu ƙananan sana’o’i.

A tare da haka kuma a samar da tsare tsare na gaggawa na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, kamar wanda shugaba Buhari ya ɗauka a farkon kama mulkinsa na samar da kuɗaɗen tallafi ga jihohi don shawo kan matsalar basussukan albashin ma’aikata da sauran matsalolin cikin gida. Tattalin arzikin Nijeriya na cikin wani hali, kuma ya kamata a yi da gaske wajen bunƙasa shi, domin rayuwar talaka ta inganta.

Batun albashin ma’aikata na daga cikin muhimman abubuwan da sabuwar gwamnati ya kamata ta kalla, lallai ma’aikacin gwamnati a Najeriya yana ganin tasku, rayuwa ta yi tsada sosai, kuma albashinsa bai taka kara ya karya ba. Idan gwamnati mai zuwa na son ganin farin cikin ‘yan Najeriya da samun goyon bayan su to, lallai ta yi wani abu cikin gaggawa don ganin ta qara albashin ma’aikata da inganta tsarin aikin gwamnati, domin a samu sassauci daga ƙuncin da ma’aikata ke ciki.

Kada sabuwar gwamnati ta shagala da murna da jin daɗin karɓar mulki ta manta da batun matsalar tsaro da ke addabar jama’a a ƙauyuka da birane da manyan hanyoyin ƙasar nan. Lallai kada a ɗauki lafawar al’amura a watannin baya bayan nan a matsayin mutuwar damuwar ne, a’a, sam ba haka ba ne. ‘Yan ta’adda na nan sun yi lamo ne suna nazarin al’amura, ga batun ƙananan makamai da suka yi yawa a hannun jama’a, waɗanda wajibi ne jami’an tsaro su binciko inda suke da hanyoyin da suke shigowa ƙasar nan, domin a daƙile su.

Harkokin kasuwanci da shigi da ficen kayayyaki, wanda a baya aka kulle su da takure shiga da fitar su lallai ne a duba yiwuwar samar da tsarin da zai magance wannan matsala da hanzari, domin a sakewa ‘yan kasuwa mara su yi kasuwanci cikin kwanciyar rai, don talaka a samu sauƙi wajen sayen kayan masarufi, da walwala a cikin ƙasa.

Harkar ilimi, kiwon lafiya da makamashi na daga cikin muhimman ɓangarorin da ke buƙatar ceto na gaggawa, don ceto rayuwar ‘yan Nijeriya da matasa, wajen samar da ayyukan yi ga matasa, dawo da kimar cibiyoyin lafiya da qara darajar manyan makarantu da ƙanana mallakin gwamnati, domin ‘ya’yan talakawa su samu ilimi ingantacce, kuma su ba da gudunmawa ga cigaban ƙasa.

Ba ma sa ran gwamnati mai zuwa za ta ja kafa wajen naɗe-naɗen muƙamai da daidaita tafiyar sabuwar gwamnati cikin taƙaitaccen lokaci, ba kamar yadda gwamnati mai ci ta yi jinkirin samar da ministoci da masu dafa mata wajen tafiyar da al’amuran mulki ba. Lallai a ja kowanne ɓangaren ƙasa cikin harkokin tafiyar da gwamnati, ba tare da an manta da waɗanda suka yi wahalar kafa gwamnati da taya ta yaqin neman zaɓe ba, ko kuma nuna wariya da fifita ‘yan wani ɓangaren wajen samun damammaki a cikin gwamnati.

Muna taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasa da mataimakinsa murna, tare da tuna musu cewa, wannan nauyi ne da Allah ya ɗora musu don ya ga yadda za su cika alƙawuran da suka yi wa jama’a, kada su watsawa talakawan da suka kawo su kan mulki ƙasa a ido, su yi abin da ya dace, don ƙasa ta samu lafiya da cigaba.