Zaɓen 2023: Ana yi wa Tinubu kutingwila a Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A wani yanayi mai nuna alamun kutingwila ga lashe zaɓen 2023 da zavavven Shugaban Ƙasa mai jiran gado a Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi, wasu ’yan Nijeriya da dama mazauna Birnin Landon, Babban Birnin Ƙasar Ingila, sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a gaban ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar dake birnin Landan ɗin na ƙasar Birtaniya.

Wannan ya faru ne jim kaɗan bayan Chatham House ya soki lamarin yadda aka tattara sakamakon zaɓen, wanda ya bai wa Tinubun nasara, inda gidan na dimukraɗiyya ya ce, ba a bi qa’idojin zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a Nijeriya (INEC) ta saka ba.

Zanga-zangar, wacce aka gudanar a jiya Alhamis, 9 ga Maris, 2023, ta kasance qarqashin jagorancin tsohon Kakakin Shugaban Ƙasa, Mista Reno Omokri.

Jama’ar sun nuna fushinsu ne da rashin jin daɗin yadda hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta gudanar da zaɓen, inda suka buƙaci a soke Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu.

Da yake jawabi a wajen taron, Mista Omokri ya bayyana cewa, daga na’urar tashar IREV ta hukumar zave ta INEC, an ga ƙuri’u kusan 14,000, wanda ya shafi ƙuri’u miliyan 4.3, kuma an gudanar da tantancewar da hannu a waɗannan rumfunan zaɓe da sauran su, wanda ya saɓa wa sashi na 47 (47). 2) da (3) na dokar zaɓe.

Ya ce, bisa ga waɗancan sassa na dokar, kamata ya yi a soke zaɓe a waɗannan yankuna kuma a gudanar da shi a ranar ƙarshe.

Da yake kira da a soke zaɓen domin samun sahihin zace, Omokri ya ce, “Babu shakka INEC ba ta shirya ba, amma duk da haka ta ci gaba da zaɓen a makance wanda hakan ya baiwa jam’iyya mai mulki damar yin amfani da dabara wajen maguɗin zaɓe.”

Ya ci gaba da cewa, “Hukumar INEC ta ɗage zaben gwamna ne saboda ba su shirya ba, abin da ya kamata su yi kenan zaɓen shugaban ƙasa idan ba su da wata ɓoyayyar manufa.”

Da yake jawabi ga gungun masu zanga-zangar, Fasto Omokri ya ce, zanga-zangar ba ta wata jam’iyya ba ce, a’a, tsarin bai ɗaya ne na neman zaɓe na gaskiya da adalci daga INEC ga ɗaukacin ’yan Nijeriya.

A cewar Omokri, Nijeriya a matsayinta na babbar nahiyar Afirka ya kamata ta jagoranci sauran ƙananan ƙasashen Afirka da sahihin zaɓe. Sai dai kuma abin takaicin shi ne, ƙananan ƙasashen Afirka ne ke gudanar da sahihin zaɓe yayin da a kullum zaɓe a Nijeriya ke cike da al’amura da dama kamar maguɗi, tashe-tashen hankula, sayen ƙuri’u, da kuma fitowar ’yan takara suna neman ƙuri’a da ƙarfi daga wajen mutane.

Ya ce, “Ƙasashen Afirka da ke da ƙarancin ƙuri’u sannan kuma ƙuri’unsu na tafiya yadda ya kamata. Sannan muna da namu ƙuri’a sannan muna da dukkan waɗannan batutuwa. Babu wata ƙasa ko wata cibiya zaya a wajen Nijeriya da ta ce zacen ya yi kyau.

“Kwanaki da suka wuce Chatham House ta ce zacen bai cika ƙa’idojin da ake buƙata ba. Jakadan na Amurka ya ce wannan zaɓe bai dace da abin da ’yan Nijeriya ke zato ba.”

idan za a iya tunawa, a ranar Juma’a, 3 ga Maris, 2023, magoya bayan ɗan takarar Jam’iyyar LP, Peter Obi, sun gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin Nijeriya dake Landon ma, inda suka buƙaci a soke zaɓen Tinubu kuma a maye gurbinsa da nasu gwanin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *