Zaɓen 2023: Atiku ya nesanta kansa da wani shirin kamfe

Daga WAKILINMU

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nesanta kansa da wani shirin yaƙin meman zaɓe inda aka haɗa hotonsa da na tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mr Charles Soludo.

A Litinin da ta gabata aka ga fostoci ɗauke da hoton Atiku da Soludo na ta karkaina a birnin Abuja a matsayin ‘yan takarar shugaban ƙasa ya zuwa babban zaɓen 2023.

Cikin sanarwar da hadiminsa kan sha’anin yaɗa labarai, Paul Ibe ya fitar, Atiku ya ce ba shi da masaniya a kan waɗannan hotuna da ake yaɗawa kuma ya nesata kansa da hakan.

A cewar sanarwa, “Hankalinmu ya kai kan wasu rahotanni da aka yaɗa a wasu kafafen yaɗa labarai game da takarar Mai Girma Atiku Abubakar da Farfesa Charles Soludo a matsayin ɗan takarar gwamna na Jihar Anambra da aka yaɗa a sassan Abuja.

“Hasali kamata ya yi mu kau da kai daga rahotannin amma gudun a ɓatar da wasu da shirin, ba mu san komai ba dangane da hotunan da aka yaɗa ko waɗanda suka yaɗa shirin.

“A bayyane yake wannan aikin mahassada ne. Domin kawar da kokwanto a zukatan mutane, Atiku ɗan PDP ne shi kuma Soludo ɗan APGA. Rashin kan gado ne ga duk wanda ya saka Atiku cikin sha’anin zaɓen Anambra wanda jama’ar jihar ne kaɗai za su tabbatar da sakamakonsa.”

Da wannan sanarwar ta buƙaci jama’a da su yi watsi da wannan batu, tana mai cewa ƙulle-ƙullen mahassada ne kawai amma babu ƙamshin gaskiya cikinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *