Zaɓen 2023 da kamar wuya muddin ba a magance matsalar tsaro ba – Ejiofor

Daga UMAR M. GOMBE

Tsohon Daraktan Sashen Tsaron DSS, Mike Ejiofor, ya ce duba da yadda fannin tsaron ƙasar nan ke ta sukurkucewa ya sa yake ganin da kamar wuya a iya gudanar da zaɓuɓɓukan 2023.

Ejiofor ya yi wannan bayani ne yayin hirar da aka yi da shi a tashar Channels a ranar Litinin.

Ya ce tun dare bai yi mata ba ya kamata Gwamnatin Tarayya ta gaggauta ɗaukar matakin daƙile wannan matsalar da ta yi wa ƙasa tarnaƙi.

Yana mai cewa, “Muddin ba a magnace matsalar tsaron da ta addabi sassan ƙasa kafin zaɓuɓɓukan 2023 ba, ina mai bada tabbacin cewa zaɓe ba zai yiwu ba.

“Za a samu tashin-tashina a wannan ƙasa. Akwai buƙatar a daidaita komai kafin 2023.

“Mu sanya batun ƙasa a gaba kafin a zo kan batun zaɓuɓɓuka. Idan kuwa muka ci gaba a haka ba za mu iya gudanar da zaɓe ba saboda yawan tashin hankali.”

Ejiofor ya ce ganin yadda matsalar tsaron ƙasar nan ta ta’azzara, shi ma ya goyi bayan kiraye-kirayen da aka yi kan cewa a sake wa ƙasa fasali, saboda a cewarsa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin ƙasa da daman gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *