Zaɓen 2023: Ban janye daga takarar Gwamnan Yobe a PDP ba – Hon. Shariff

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Yobe a ƙarƙashin Jam’iyyar PDP, a zaɓen 2023 mai zuwa, Hon. Shariff Abdullahi ya ƙaryata jita-jitar janye takararsa tare da mayar da martanin cewa wannan farfaganda ce maras tushe da makama.

Ya jadada cewa babu wannan magana; ba a yi ta ba kuma babu alamarta, face kawai ƙarya ce tsagwaronta wadda wasu maras tunani suka ƙirƙira tare da yaɗa ta domin sanyaya gwiwar magoya bayansa.

Hon. Shariff Abdullahi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar manema labaru mai ɗauke da sa hannunsa, wadda aka raba wa ‘yan jaridu ranar Litinin a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Yayin da sanarwar ta ƙara da cewa, abin da masu iri-iren wannan gutsiri-tsoma ba su sani ba shi ne, PDP jam’iyya ce mai tsari kuma mai haɗin kai tare da bin dokoki sau da ƙafa, wannan yunƙurin bai gaza shure-shure baya hana mutuwa ba.

“A hannu guda kuma, idan abin a tambayi masu yaɗa wannan ƙaryar ne; shin idan takara zai janye takararsa a daidai wannan lokacin, shin akwai damar sake wani zaɓen fidda gwani, ko a haka wanda aka janye wa zai shiga babban zaɓe?

Sannan anya masu yaɗa wannan farfagandar sun karanta dokokin zaɓe na 2022, tsare-tsare da tanade-tanaden da suka kafa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC)?

“Saboda haka, babu inda na bayyana hakan a rubuce, kuma ban yi zancen da kowa ba kan cewa zan janye ba, ba a yi wannan ba kuma halin da ake ciki babu wannan batu.

“Kuma idan PDP za ta sauya ɗan takaran da ya ci zaɓen fidda gwani sai ta ɗauko wani can daban wanda, ɗan APC ta bashi takarar, alhalin tana da waɗanda suka shiga zaɓen fidda gwanin dani; ai idan ma hakan ne ɗayansu ya cancanta. Kuma kuna ga zai yuwu ɗan siyasa Irina zai janye takarar ba tare da tuntuɓar al’umma ta ba”?

Hon. Shariff ya bayyana ya yi kira ga al’ummar jihar Yobe, musamman ‘yan Jam’iyyar PDP su yi watsi da wannan ƙarya maras tushe. Tare da jaddada cewa zai ci gaba da riƙe amanar da suka damƙa masa ta takarar Gwamnan Jihar Yobe a zaɓe mai zuwa a 2023 in sha Allah. Kuma ya ce cikin yardar Allah Jam’iyyar PDP ita ce da nasara saboda su suke da cikakken goyon bayan Jama’a.

“Sannan kuma Ina ƙara kira ga al’ummar jihar Yobe baki ɗaya, musamman ‘yan Jam’iyyar PDP mu ci gaba da juriya da cikakken haɗin kai, saboda sai ta haka za mu samu nasara.

“Kuma ya na daga cikin burinmu samun cikakken haɗin kan baki ɗayan al’ummar jihar Yobe, za mu yi aiki da kowa wajen ganin mun sake farfaɗo da jiharmu wajen magance ƙalubalen da mu ke fuskanta, wanda sanin kowa ne cewa al’ummar jihar Yobe suna da buƙatar canjin gwamnati, saboda yadda APC ta dagula al’amurra tare da mayar da hannun agogo baya.

“Ci gaban Jihar Yobe zai yuwu ne ta hanyar haɗa hannu da ƙarfi, mutunta juna, wanda ko shakka babu muna da manyan ƙalubalen da ya dace mu fuskanta wanda bisa ga hakan ne muke ci gaba da aiwatar da ingantattun tsare-tsare da shiri mai ma’ana wajen tunkarar su.

“Muna da ƙwarewar da za mu sake gina jiharmu; ba zance ne na ɓaɓatu da faɗa a baki ba, abu ne a bayyane; zo ka nuna mana abin da ka taba yi wa al’ummar jihar Yobe, amma ba ka shigo ka yi surutu ka gudu ba. Ko a zaɓe ka ka gudu sai bayan wata ɗaya ko biyu ba, ko sai lokacin zaɓe ka zo,” inji shi.

Ya ce lokaci ya yi wanda al’ummar jihar Yobe za su bambance ɗan duma da na kabewa, saboda yanzu duniya ta na ƙarni na 21 ne, zamanin ci gaba wanda shugaba zai baje kolin ƙwarewarsa da ilimi, ba a siffar ‘yan daba ba.

Ya ce bai dace al’ummar Yobe su sauraron ‘yan siyasa masu kama da ‘yan sara-suka ba, mayun mulki, ‘yan ta yi-daɗi, ‘yan siyasar da ba a ganin fuskokin su sai lokacin zaɓe; bayan sun karvi kwangila su zo domin yi wa jama’a burga. Daga nan ba a qara jin muryarsu sai bayan shekaru huɗu.

“Insha Allah muna ƙara tabbatar wa da al’ummar jihar Yobe cewa muna nan kan bakarmu kuma da yardar Allah za mu cire jaki daga cikin gonar duma,” ta bakin Hon. Abdullahi.

A ƙarshe ya bayyana ya miƙa saƙon godiya ga shugabannin Jam’iyyar PDP a jihar Yobe da na ƙasa baki ɗaya, ƙusoshin jam’iyyar, ‘yan takara a kowane mataki a nan jihar Yobe da ƙasa baki ɗaya, dattawan PDP, matasa maza da mata da ɗaukacin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP da al’ummar jihar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *