Zaɓen 2023: Hukumar NDLEA za ta yi wa ‘yan takara gwajin ƙwaya

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gabanin zaɓen gamagari na shekara ta 2023, shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya-Janar Buba Marwa ya rubuta wa shugaban jam’iyyar APC dake riƙe da madafun mulki, Sanata Abdullahi Adamu da buƙatar yin gwajin mutumtaka wa masu son tsayawa takarar neman zaɓe mai gabatowa.

Marwa ya kuma bayyana cewar, zai rubuta wa shugabannin babbar jam’iyyar adawa ta PDP makamancin wancan buƙata na gwajin samfurin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi akan dukkan mamban jam’iyya dake sha’awar shiga takarar zaɓe, musamman masu harin riƙe manyan kujerun mulki.

Da yake yin jawabi a wajen taron karramawa ma’abuta cancanta daga cikin ma’aikatan hukumar na rubu’in farko na wannan shekara, shugaban na NDLEA ya bayyana cewar, gwajin tantance samfurin gwayar yana da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da cewar, ‘yan siyasa da aka ɗorawa haƙƙin gudanar da ofisoshin mulki ba su yi amfani da kuɗaɗen jama’a ba wajen sayen ƙwayoyi kamar su Cocaine da Methamphetamine a maimakon yi wa jama’a aiki.

Janar Buba Marwa ya kuma bayyana cewar, yin ta’ammali da ƙwayoyi ba bisa shimfiɗaɗɗun qa’idojin kiwon lafiya ko na likita ba, shine babban ummul-aba’isun ɓarkewar rashin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar nan, don haka ya zame wajibi doka ta fara aiki tun daga cikin gida.