Zaɓen 2023: Lokacin huce haushin talaka

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kusan kowa a ƙasar nan, a kusa yake! Ma’ana a cikin fushi ko matsuwa yake, saboda yadda abubuwa suke tafiya a ƙasar nan. Hatta waɗanda suka taka wani mataki a Tudun Mun Tsira da waɗanda ke kusa da gwamnati, su ma ba lallai suna ganin yadda suke so ba. Rayuwa ta zama wani iri, ‘yan Nijeriya sun samu kansu a wata irin rayuwa marar tabbas! Rashin tabbas ya zama shi ne kaɗai tabbas a ƙasar nan!!

Ƙarfi da yaji talaka ya koyi wata irin rayuwa da a baya bai san da ita ba, wani ma ko a mafarki aka ce masa zai ga irin wannan sauyin yanayi zai yi musu, saboda yadda yake ganin komai na rayuwarsa na tafiya daidai da tsarin da ya shiryawa kansa.

Gwamnati a kodayaushe cewa take yi tana iyaka bakin ƙoƙarin ta don daidaita al’amura, kuma tana fitar wasu tsare-tsare na sassauta tsananin da talakan qasar nan ke fuska. Yayin da miliyoyin kuɗaɗe ke sulalewa da sunan tallafin rage kaifin talauci, don tallafawa masu ƙananan sana’o’i da matasa marasa ayyukan yi.

Sai dai ina wannan tallafi yake tafiya? Anya ana ba da shi a yadda gwamnati take ayyana bayarwa? Sana’o’in da aka ce ana koyarwa da tallafin da ake bayarwa da nufin ƙananan jari, suna isa ga waɗanda ake nufin a bai wa? Wanne sa ido da babiya gwamnati ke yi don ta tabbatar ta cika alƙawarin da ta yi wa talakawa? Abubuwa da yawa fa ba sa tafiya daidai!

Wanne darasi gwamnati da sauran hukumomin da ake bai wa alhakin raba tallafi da ayyukan jin ƙai suka koya daga boren da talakawa suka yi a lokacin zaman gida na Korona, inda aka farfasa rumbunan adana kayan abinci da aka shirya rabawa talakawa, amma aka karkatar da su, don biyan wasu buƙatu na son rai.

Wanne tabbaci ake da shi na cewa, irin haka ba za ta iya sake faruwa ba idan kunci ya yi wa talakawa yawa? Lallai ne gwamnati ta riqa tanadar matakai na dakushe zargi da yawan vata mata suna da ake yi, saboda yadda wasu da ta yarda da su ta ba su alhakin isar mata da saƙo ba sa yin abin da ya dace. A mafi akasarin lokuta, rijiya na ba da ruwa, amma guga tana hanawa!

Abubuwan da suke faruwa sakamakon canjin kuɗi da aka yi, da rashin samun wadatattun kuɗi na gudanar da ƙananan harkokin yau da kullum a wajen jama’a, ya ƙara tunzura jama’a suna ganin da gangan ake fito da irin waɗannan tsare tsare don a quntata musu.

A wani gefen ma har ana nuna gwamnati ko shugaban ƙasa a matsayin mutumin da ke jin daɗin ganin talaka a cikin qunci. Duk kuwa da bayanan da ya sha yi wa jama’ar ƙasa kan burinsa na ganin talaka ya samu sauqin rayuwa da adalci a ƙasar nan.

Ban da matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ake fuskanta, sauyin kuɗi da aka ɓullo da shi da rage yawan amfani da kuɗi a hadahadar mutane, ya ƙara jefa rayuwar talakawa cikin wani mawuyacin hali. Da masu kuɗin da talakawa kowa kuka ya ke yi, saboda tsayawar al’amura. Yayin da ’yan siyasa ke ƙoƙarin siyasantar da tsarin wanda gwamnati ke cewa saboda cigaban koasa ta ɓullo da shi.

Har waɗanda ke cikin Jam’iyya mai mulki ta APC kuma suke goyon bayan ɗan takarar jam’iyyar a matakin shugaban ƙasa da wasu matakai a tarayya da jihohi, suna danganta wannan canji da makircin siyasa. A cewar su, an ɓullo da tsarin a irin wannan lokaci ne don a dakushe farin jinin Jam’iyyar da kuma ɗan takarar da suke goyon baya, Sanata Bola Ahmed Tinubu.

Dama mun san ’yan siyasa, a koyaushe cikar burinsu su shi ne gaba da komai, kuma duk wani abu sa zai kawo musu cikas a zaɓe za su kawar da shi, ko da kuwa daga iyalinsu ne ko danginsu. Shi ya sa yanzu da suka ga zaɓe na gabatowa kuma talakawa sai tofin alatsine suke yi, nan da nan suka kwancewa shugaban ƙasa zani a kasuwa, suna nesanta kansu da canjin kuɗi, wasu gwamnoni ma har da zuwa kotu.

Duk da abubuwan da ke faru na tsanantar rashin kuɗaɗe da yunwa da aka shiga a ƙasa, sai gashi su ’yan siyasa suna ta walwalarsu, ana cigaba da yaƙin neman zaɓe, ana lasa wa talakawa zuma a baki, don su zaɓe su babu tausayawa ta tsakani da Allah, sai dai ta kwaɗayin neman goyon baya. Har ma da masu cewa, in sun hau mulki za su soke wannan tsari kowa ya koma amfani da tsohon kuɗi da sabo. Su kuwa talakawa babu abin da suke yi sai murna, suna ganin don su ake ƙoƙarin kafa sabuwar gwamnati.

Kodayake, ’yan siyasa na ganin talakawa kamar kaji suke, ana watsa musu tsaba shi kenan. Don haka sun bi sun kwashe sabbin kuɗaɗe a bankuna sun ɓoye sai lokacin zaɓe ya yi za su fito da su suna sayen ra’ayin talakawa, saboda a lokacin an shiga ƙangi, ganin sabon kuɗi ba, rahama ce a gun talaka, ko da nawa zai samu, ba zai damu ba, in dai ’yan canji za su shigo hannunsa.

Saboda a takure yake, iyalinsa na jiran ya nemo ya kawo gida! Duk kuwa da yadda ake samun wasu da ke cewa sun fitar da rai daga samun canji a ƙasar nan, ko samun shugabanni nagari, don haka ba su babu ƙara jefa ƙuri’a. Wasu kuma na ganin tun da ba son ran su shi ne zai kawo canji ba to, gara ko nawa aka ba su su karɓa, don su rage asara, dama can dukiyar ƙasa ce aka sace.

To, ni dai abin da zan gaya wa talakan Nijeriya shi ne yanzu ne lokacin da ya fi dacewa ya fita ya yi zaɓe, kuma ya tabbatar abin da yake so shi ya zaɓa ba tare da biye wa wani abin duniya ya canja masa tunani ba, ya zaɓi waɗanda zuciyar sa ta fi natsuwa da za su kwatanta masa adalci.

Ya huce haushin sa ta hanyar amfani da katinsa na zaɓe wajen tabbatar da ganin tsofaffin ’yan siyasar da a baya suka yaudare shi ba su tsinana komai na kawo wa talaka sauqi ba, sun yi waje, ya zaɓi waɗanda za su iya riƙe amana, kuma su kawo gyara.

Mu tabbatar katinan zaɓen mu na kusa, ta yadda lokaci na yi za mu dauko su, mu je mu yi zaɓe, kuma mu yi addu’a, Allah ya sa waɗanda za su hau karagar mulki a matakai daban-daban, sun zo da niyyar alheri, sun zo da shirin kawo gyara, ba arzuta kansu da satar dukiyar ƙasa ba.