Zaɓen 2023: Waɗanne abubuwa ne suka fi ɗaukar hankalin masu zaɓe?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Komai aka sa masa lokaci zai zo ya wuce, in da rai da nisan kwana. Babban Zaɓen 2023 da ake ta dakon zuwansa ana ta shirye-shirye a matakai daban-daban ya zo ya wuce, cikin lumana da kwanciyar hankali, duk da ƙalubalen tsaro da aka fuskanta nan da can. An yi nasarar kammala zaɓen Shugaban Ƙasa da na ’yan Majalisar Ƙasa, yayin da aka yi na Gwamna da na ’yan Majalisar Jiha.

Sai dai duk da kasancewar an yi zaɓe cikin lumana a mafi akasarin jihohin ƙasar nan musamman a nan Arewa. Ba za a rasa wasu darussa da ya kamata mu ɗauka su zame mana darasi ba, waɗanda idan mun riƙe su za su taimaka mana mu inganta harkokin zaɓen mu na gaba, don bunqasa mulkin dimukraɗiyya da cigaban ƙasa.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke shirin barin mulki cikin kyawawan abubuwan da ya ce yana so a riƙa tunawa da shi bayan saukar sa sun haɗa da batun inganta tsarin gudanar da zaɓe, da hana amfani da kuɗi a lokacin zaɓe. Don haka ne ma a cikin matakan da ya ɗauka har da batun canza kuɗi, da taƙaita amfani da tsabar kuɗi a cinikayya. Wanda hakan na da nasaba da ƙoƙarin hana fitar da kuɗi wajen sayen ƙuri’u, abin da ’yan siyasa da sauran ’yan Nijeriya suka yi yaƙi da shi, saboda yadda wannan tsari ya jefa rayuwar su cikin ƙunci da rashin tabbas.

Sai dai bisa nazari da na yi kan abubuwan da suka gudana a lokacin zaɓukan da suka gabata, batun sayen ƙuri’u ya taka gagarumar rawa wajen canja ra’ayin mutane. Saboda yadda jama’a suka shiga tsananin rashin kuɗaɗen gudanar harkokin su, ya sa sun miqa wuya ga tarkon ’yan siyasa, waɗanda su kuma suka yi amfani da damar su wajen saye sabbin kuɗaɗen da aka ce an buga daga wajen manajojin bankuna, bisa zargi mafi rinjaye, don su yi amfani da su a lokacin zaɓe. A hasashena ma babu lokacin da aka yi kasuwancin sayen ƙuri’u a lokacin zaɓe a tarihin dimukraɗiyya a Nijeriya irin wannan lokacin.

Domin kuwa mun ga yadda aka riƙa fitar da sabbin kuɗaɗen nan ana rabawa talakawa ɗari biyar biyar, da dubu ɗaya don canza ra’ayin jama’a, musamman a lokacin da aka yi zaɓen Gwamna da na ’yan Majalisar Jiha.

Har a filin zaɓe, wakilan ’yan siyasa sun baza mutanen su suna leƙawa su tabbatar wacce Jam’iyya mutum ya zaɓa, sai ya je a miƙa masa abin cefane, a wani wajen ma bai kai ko ɗari biyar ɗin ba, musamman a ƙauyuka.

Da idona na shaida inda ake raba lemon kwalba ga masu zaɓe, idan ka zaɓi wanda ake so, sai ka zo a miƙa maka, saboda jami’an leƙen asiri da na hukumar yaƙi da almundahanar kuɗaɗe ta EFCC na yawo suna farautar masu sayen ƙuri’a, amma a haka aka juya kuɗaɗen zuwa kayan abinci irin su taliya, sinadarin ɗanɗanon girki, kayan shayi, and lemon kwalba da biskit, da atamfofi, akwai inda aka ce ma har da daƙwalwar kaza.

Wannan ya nuna cewa, duk ƙoƙarin da Shugaban Ƙasa ya yi na sauya yadda harkokin zaɓe ke tafiya ya tashi a banza. ’Yan siyasa da ’yan kanzaginsu sun lalata manufar, saboda burinsu na cimma nasarar da suke nema a zaɓe. Yayin da talaka ya zama shi ne a wahale, ya sha wahala wajen kai kuɗi banki don a yi masa canji, bai samu sabon kuɗin ba, ya dawo babu tsohon kuɗi babu sabo, kuma ranar zave an bi shi da taliya sunƙi ɗaya da fallen zani, a matsayin diyyar wahalar da aka jefa shi a ciki.

Tsare tsaren da aka ɗauka tsakanin gwamnati da hukumar zaɓe ta INEC, da jami’an tsaro, duk ba su yi tasirin da ake buƙata ba, a wannan ɓangaren, dole hukumomi da masu ruwa da tsaki su yi nasu tanadin don ganin an tsamo talaka daga irin wannan rayuwa ta rashin daraja ’yancinsa da zaɓinsa.

Akwai kuma wani vangare da shi ma ya taka rawa sosai a lokacin wannan Babban Zaɓe, shi ne kuwa amfani da makamai da ’yan daba, wajen far wa abokan adawa, abin ya yi muni sosai a wannan karon.

A jihohin Kano, Legas, Katsina, Zamfara, Inugu da Imo da sauran wuraren da ake samun ’yar tsama tsakanin gwamnati mai ci da ’yan adawa masu niyyar karvar mulki da ƙarfin ƙuri’a. Amfani da ’yan daba ko ’yan tsagera ba sabon abu ba ne a siyasar ƙasar nan, amma a wannan lokacin ya ƙara tsananta, saboda yadda aka nuna siyasar addini, ƙabilanci, da kuma ɓangaranci, a cikin ƙasa da ma cikin jiha.

Wata ƙungiya mai nazarin harkokin dimukraɗiyya ta CDD ta fitar da rahoton cewa a tsakanin watanni uku na farkon wannan shekara an kashe mutane 109 da ke da alaqa da siyasa da batun zaɓe. Rigimar ’yan daba tsakanin magoya baya ta kafin zaɓe da bayan zave ta haifar da asarar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa.

Kamar misalin Jihar Kano inda aka kama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai ta Tarayya, Honarabul Alhassan Ado Doguwa ana zargin sa da hannu wajen kisan kai da tunzura magoya baya su yi ƙone-ƙone a yankin da yake wakilta na Tudun Wada da Doguwa. Da kuma ɓarnar da aka ce an tafka wa fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Kahutu Rarara, bayan sanar da nasarar Jam’iyyar NNPP a Kano, sakamakon irin waƙoƙin da yake yi wa jam’iyyar da yake goyon baya ta APC, da zargin da ake yi na cewa yana gugar zana wa ’yan adawa.

Wannan ya sa wasu tsagerun matasa far wa gidansa da yi masa ɓarna, yayin sauran jama’a ke bin hanyar lumana wajen nuna farin cikinsu.

Akwai rahotanni da suka bayyana cewa, jami’an tsaro sun kama wani shugaban hukumar sufuri ta Jihar Kano, wanda jami’an tsaro suka kama bisa zargin hayar ’yan daba da za su tarwatsa cibiyoyin zaɓe da hana mutane zaɓin da suke so, don kada ɗan takarar gwamnatin Kano ya faɗi zaɓe.

Yadda ’yan siyasa suka ɗauki siyasar ko a mutu ko a yi rai, abin tada hankali ne sosai da fargaba. Saboda in har yanzu ba mu canja tunanin mu kan yadda muke ɗaukar siyasa ba to, babu shakka akwai babbar matsala a gaba.

Abu na gaba da na yi la’akari da tasirin sa a waɗannan zaɓuka da suka gabata shi ne, tasirin addini da malamai wajen juya akalar ’yan siyasa ko masu zaɓe. Malaman addini daga ɓangaren Musulmi da Kirista sun mayar da wuraren wa’azi tamkar dandalin kamfen, inda ɓaro-ɓaro za ka ji malami ko fasto na bayyana inda ya fuskanta a siyasarsa, ko wanda yake so magoya bayansa su zaɓa saboda maslahar addini ko ta ƙashin kansa.

A wannan shafin mun sha tattauna batun illar da shigar da addini cikin siyasa yake da shi, musamman ƙalubalen da hakan ke haifar wa wajen raba kan jama’a da haifar da rashin zaman lafiya. Yana kuma tunzura mutane su haɗa kai don adawa da ɗaya ɓangaren addini, a bisa tunanin za a yi musu danniya ko tauye musu haƙƙi da sunan addini. Kamar yadda ta faru a Jihar Filato da Jihar Kaduna, jihohin da dama sun yi ƙaurin suna kan rigingimun addini da ƙabilanci.

Zaɓen da ya gudana a jihohin nan ya fi kama da zaɓen addini fiye da na siyasa, wanda kuma hakan ba ya rasa nasaba da wasu maganganu da aka naɗa kuma aka riƙa yaɗa su a wayoyin jama’a da ke nuna inda wasu malaman addini ke fifita wani ɗan takara ko vata sunan wani ɗan takara.

Lallai ne a kawo ƙarshen irin wannan matsalar wacce a maimakon kare martaba da mutuncin malaman tana jawo musu baƙin jini ne da zubar musu da kima a idon wasu mutane. Ya kamata malamai su zama iyayen al’umma, su ɗauki kowanne ɓangaren siyasa nasu ne, a daina taya ’yan siyasa kamfen a wuraren ambaton Ubangiji. A tsarkake sunan Ubangiji, a girmama sunansa, a ja hankalin jama’a zuwa ga haɗin kai da zaman lafiya.

Abu na ƙarshe da na yi la’akari da shi a wannan Babban Zave har wa yau shi ne shigar matasa cikin takara, musamman a zaɓen majalisar dokoki ta jiha. Akwai rahotanni da ke bayyana cewa, wasu matasa sun yi rawar gani wajen samun damar ƙwace wasu muhimman kujeru a hannun tsofaffin ’yan siyasa ko wasu da ake ganin sun jima ana damawa da su.

Happiness Akawu mai shekaru 35 ta samu nasarar kayar da Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Filato, Honarabul Yakubu Sanda, a mazaɓar Pengana, ƙarƙahin Jam’iyyar PDP. Haka kuma wani matashi Lawal Musa wanda ya kasance malamin makaranta ne daga yankin Nguru na Jihar Yobe shi ma ya samu nasarar ƙarƙashin Jam’iyyar PDP inda ya kayar da dattijo, Honarabul Ahmad Lawal Mirwa, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar na Jam’iyyar APC, wanda bayanai ke nuni da cewa, sau shida ana zaɓarsa a wannan kujera.

A Jihar Kwara ma, Rukayyat Motunrayo Shittu mai shekaru 25 ta samu nasarar shiga Majalisar Dokoki ta Jihar a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, wacce ita ce ’yar majalisa mafi ƙarancin shekaru a jihar. Ga kuma Zinariyar Saminaka, Munirat Suleiman Tanimu da aka zave ta don ta wakilci yankin Lere ta Gabas a Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna, a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, ita ma ta zama mafi ƙarancin shekaru da za ta shiga majalisar jihar.

Waɗannan kaɗan ne daga cikin matasan da suka taka rawar gani a wannan Babban Zaɓen 2023 da ya nuna lallai matasa sun samu ƙwarin gwiwa, kuma sun yi shirin shiga a dama da su don samun damar kawo canji da cigaba a siyasar Nijeriya.