Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Jam’iyyar Labour Party (LP) mai adawa a zaɓen Shugaban Ƙasa na Nijeriya ta bayyana cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na Jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.
Yayin da yake jawabi a Abuja a ranar Laraba, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Datti Baba Ahmed, ya jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen.
“Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP,” a cewarsa. “Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP”.
Tun a ranar Talata jam’iyyun adawa na PDP da LP da ADC suka yi watsi da sakamakon a wani taron haɗin gwiwa, suna masu cewa hukumar zaɓe ta INEC ta gaza saka sakamakon a rumubun IReV da zai sa a gan shi ta shafin hukumar na intanet.
Peter Obi na LP ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 4,223,277, inda Atiku Abubakar na PDP kuma yake biye wa Tinubu da ƙuri’u 6,301,741.