Zaɓen 2023: Zan yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa nagartar Jihar Neja – Malagi

Daga WAKILIN MU

Ɗaya daga cikin manyan masu neman tsaya wa jam’iyyar APC takarar zama gwamna a Jihar Neja, Alhaji Mohammed Idris Malagi, ya sha alwashin zai fara aiki daga sa’ar farko da ya kama aiki a matsayin gwamna domin cimma burin sa na gina sabuwar nagartacciyar Jihar Neja idan har aka ba shi damar zama ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen fidda gwani mai zuwa.

Malagi, wanda shi ne Shugaban kamfanin buga jaridun Blueprint da Manhaja, ya faɗi haka ne a ranar Talata a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan ya miƙa fom ɗin sa na shiga takara ga shugabannin APC a Cibiyar Tarurruka ta Duniya da ke Abuja.

Ya ce ya tsara shirin sa na haɓaka Neja ne a bisa kyakkyawan ginshiƙin da ke akwai a yanzu a jihar.

Ya ƙara da cewa babu shakka Neja na daga cikin manyan jihohin da ake da su a Nijeriya idan aka yi la’akari da yawan albarkar ɗan’adam da ma’adinai da ta ke da su, sannan ya yi alƙawarin zai yi amfani da ƙarfin jama’ar jihar wajen ɗaga Neja zuwa matakin a zo a gani a tsakanin jihohin Nijeriya.

Malagi, wanda kuma ya ke riƙe da sarautar Kakakin Nupe, ya ce: “Hanyar da za mu bi mu haɓaka Jihar Neja a bayyane ta ke, babu tababa. Tun daga awa ta farko da na kama aiki a matsayin gwamnan Jihar Neja zan yi aiki da manyan albarkatun da mu ke da su na jama’a, maza da mata, da matasa masu ilimi da marasa ilimi, manoma da masu sana’o’i daban-daban, da ma kowa da kowa da ke zauna a dukkan sassan jihar don su zama duk abin da su ke su zama a ƙarƙashin yanayi na kwanciyar hankali da lumana.

“Buri na shi ne in yi aiki da nagartaccen ginshiƙin da mu ke da shi da kuma albarkatun da Allah ya ba mu na jama’a a matsayin mu na jiha wajen buɗo ƙarfin mu a ɓangarorin ilimi da aikin gona da kimiyya da fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire domin maida Neja babbar jiha ta kowace fuska. Saboda haka, ina kira ga deleget ɗin mu da dukkan ‘yan jam’iyyar mu na APC da su goyi bayan shirin da na yi domin mu yi aikin gina babbar Jihar Neja.”

Kakakin Nupe ya bada tabbacin cewa takarar sa a ƙarƙashin inuwar APC za ta tabbatar da nasara ga jam’iyyar a zaɓen gwamna da za a yi a Jihar Neja a cikin 2023.

Malagi dai mamallakin kafafen yaɗa labarai ne da su ka haɗa da gidan rediyon WE FM da ke Abuja, kuma masani ne a fannin hulɗa da jama’a.

A yayin da ya ke magana kan ƙalubale daban-daban da jihar ke fuskanta, Malagi ya ce: “Mun yi nazarin dukkan su, kuma za mu baje su baki ɗaya a faifai, mu magance su domin alfanun al’ummar mu, da alfanun gwamnatin mu, da kuma alfanun Nijeriya baki ɗaya.

“Za mu ƙara ƙarfafa Nijeriya, za mu ƙara ƙarfafa Jihar Neja, da yardar Allah.

Daga hagu: Alhaji Mohammed Idris Malagi, mai neman takarar zama gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Neja, ya na miƙa fom ɗin sa ga Alhaji Suleiman Argungu, Sakataren Tsare-tsare na APC na Ƙasa, a Cibiyar Tarurruka ta Duniya da ke Abuja, a ranar Talata

“Mun yi shirye-shirye da dama a kan batun tsaro. Kun san Jihar Neja ta na ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da babbar matsala game da tsaro. Mu na da babban tsari da mu ka yi wa matsalar. Za mu yi aiki tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, da haɗin gwiwa da sauran gwamnatocin jihohi, da kuma haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen tabbatar da cewa zaman lafiya ya dawo ga al’ummar mu, zaman lafiya ya dawo ga jihar mu, zaman lafiya ya dawo ga Nijeriya.”

Da aka yi masa tambaya kan yiwuwar sa ta samun tikitin tsaya wa jam’iyyar takara, sai Kakakin na Nupe ya kada baki ya ce: “Ina da tabbaci, ina jin ƙarfi a rai na. Kun dai ga na san zan yi nasarar samun wannan tikiti. ‘Yan Nijeriya da al’ummar Neja sun yarda da ni. Kun ga yadda aka nuna mani tun daga yadda su ka rako ni zuwa wannan wajen. Za mu samu nasarar karɓar wannan tikiti. Ina da matuƙar fatan haka. Ina jin ƙarfin hakan a rai na.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *