Zaɓen Adamawa: IGP ya canja Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da zaɓen jihar

Babban Sufeton ‘Yan Sanda (IGP), Usman Baba, ya ba da umarnin janye Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da sha’anin zaɓe a Jihar Adamawa, Mohammed Barde.

Manhaja ta gano cewar IGP ya sake ba da umarnin gaggawa a kan Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Jihar Gombe, CP Etim Equa, ya koma Adamawa da aiki don ci gaba da lura da sha’anin zaɓen gwamnan jihar wanda bai kammala ba.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce IGP na bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da komai ya gudana cikin nasara.

A cewarsa, “IGP ya ba da umarnin janye Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da zaɓen Jihar Adamawa, CP Barde, sannan takwaransa na Jihar Gombe, CP Etim Equa, ya tafi ya maye gurbinsa wajen ci gaba da lura da sha’anin zaɓen jihar.”

Adejobi ya ce kawo yanzu IGP bai samu wata wasiƙa daga Hukumar Zaɓe (INEC) ba na neman a binciki tare da hukunta Kwamishinan Zaɓen Jihar Adamawa, Hudu Yunusa Ari, kan abin da ya aikata na bayyana wanda ya lashe zaɓen Gwamnan jihar ana tsaka da tattara sakamakon zaɓe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *